Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
EndSars: An sanya dokar hana fita a Lagos
Gwamnatin Legas da ke kudancin Najeriya ta sanya dokar hana fita ta sa'a 24 a dukkanin sassan jihar bayan da zanga-zangar EndSARS ta rikide ta koma tarzoma.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya ce dokar za ta fara aiki daga ƙarfe 4 na yammacin yau.
A jihar ta Lagos aka somo zanga-zangar ta EndSARS wadda aka kwashe mako uku ana ci gaba da yi.
"Cikin kaduwa na ga yadda zanga-zangar lumana ta #EndSARS ta rikide ta zama wani babban abin tsoro da ke barazana ga zaman lafiyar al'ummarmu. 'Yan daba da bata-gari da suka labe da sunan zanga-zangar suna kashe mutane," a cewar Gwamna Sanwo-Olu.
Ya kara da cewa: "A matsayinmu na gwamnati d ke da nauyi a kanta wadda kuma ta zage dantse kan #ENDSARS, ba za mu bari a mayar da jiharmu filn yaki ba."
Gwamnatin ta Lagos ta ce ba ta son ganin kowa a waje sai ma'aikatan da suka shafi bukatu na musamman.
Babu wanda za a bari ya fito sai dai masu ayyuka na musamman da ma'akatan gaggawa, in ji Mista Babajide Sanwo-Olu.
"A matsayinmu na gwamnati d ke da nauyi a kanta wadda kuma ta zage dantse kan #ENDSARS, ba za mu bari a mayar da jiharmu filin yaki ba.
A ranar Litinin ne gwamnatin ta Lagos ta rufe makarantu a faɗin jihar sakamakon tashin hankali da zanga-zangar EndSars ke haifarwa.
Ma'aikatar Ilimin jihar ta ce kare daliban shi ne abu mai muhimmanci, sannan an bukaci iyaye su sa ido kan inda yaransu ke shiga a wannan yanayi da ake ciki.
Tashe-tashen hankula
Jihar ta Lagos ita ce ta biyu da ta sanya dokar hana fita.
Ranar Litinin gwamnatimn jihar Edo ta sanya dokar hana fita bayan wasu 'yan daba da suk labe da sunan masu zanga-zanga sun kai hari a ofisoshin 'yan sanda da gidajen yari inda suka bukatar da mutanen da ke daure.
An samu tashe-tashen hankula a birane da dama na Najeriya yayin da zanga-zangar nuna adawa da zaluncin 'ƴan sanda da ke ci gaba da gudana haifarwa.