Sudan za ta biya Amurka diyya don cire ta a jerin ƴan ta'adda

An wallafa

Amurka ta yanke shawarar cire Sudan daga cikin jerin ƙasashen da ta ayyana a matsayin ƴan ta'adda.

Amurkan ta yi hakan ne a wani mataki na ban gishiri in baka manda, wato saboda Sudan din tayi alkawarin biyan diyyar fiye da dala miliyan dari uku ga Amurkawan da aka kashe a hare-haren ta'addanci.

Shugaba Trump na Amurka ne ya sanar da wannan mataki inda ya ce za a biya diyyar ne ga wadanda suka mutu a yayin harin da ke da alaka da na kungiyar al-Qaeda wanda suka kai kan ofisoshin jakadancin Amurkan da ke Kenya da kuma Tanzania.

An kai wadannan hare-haren ne a a shekarun alif dari tara da casa'in inda aka zargi gwamnatin Sudan din da hannu a hare-haren.

Hare-haren da aka kai kan ofishin jakadancin Amurkan da Tanzania ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 220.

Wannan matakin biyan diyyar zai bude hanya ga Sudan din wajen samun kasashen waje masu zuba jari a kasar.

Shugaban ƙasar Sudan din Abdalla Hamdoki ya yi maraba da wannan mataki na Amurkan.

Ana su bangaren mahukunta a Amurkan na fatan cewa wannan yunkuri zai karfafa Sudan din ta zamo kasar Larabawa ta baya-bayan nan da zata kulla huldar diplomasiyya da Isra'ila.