Alassane Ouattara: Dole a gudanar da zabe a Ivory Coast

An wallafa

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya yi jawabi da kakkausar murya a gaban dubban magoya bayansa, inda yayi watsi da batun dage zabe da yan adawa su ka bukata.

Mr Outtara ya ce zaben shugaban kasa da a ka tsara yi karshen watannan ba bu abinda ya sauya.

Uku daga cikin abokan hamayyar shugaban sun zarge shi da saba kundin tsarin mulki bayan da ya tsaya takara a karo na uku.

A baya Alassane Outtara ya ce ba zai tsaya takara ba, to amma daga baya ya canza shawara.

Ya ce tsoron karawa da shi ne yasa yan adawa ke kame-kame.

A na tsoron barkewar rikici irin wanda ya faru bayan zaben shekarar 2010.

Kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta yamma wato ECOWAS ta ce za ta tura rundunar da za ta hana afkuwar rikici zuwa Abidjan a gobe Lahadi.

Sama da mutun 1,000 ne a ka kashe a rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a Ivory Coast na shekarar 2010.

Rikicin ya zo ne bayan da tsohon shugaba Lauren Gbagbo ya ki sauka daga mulki, a lokacin da ya sha kaye a hannun shugaba mai ci Alassane Ouattara.