Ivory Coast : Kasar ta fada rikicin siyasa

An wallafa

Dan takarar babbar jam'iyyar adawa a zaben shugaban kasa na Ivory Coast, ya yi kira da a bi duk wata hanya ta doka don dakile yunkurin shugaba Alassane Ouattara na neman wa'adin shugabanci na uku a zaben da za a yi a watan gobe.

Henri Konan Bédié, wanda tsohon shugaban kasar ne ya bayyana cewa jam'iyyun adawa sun hada kai don kare zaman lafiyar kasar.

Akalla mutane goma aka kashe tun lokacin da tarzoma ta barke a watan da ya gabata bayan Mr Ouattara ya bayyana cewa zai sake tsayawa takara sakamakon mutuwar bazata da wanda aka yi tunanin zai gaje shi yayi.

Ana ganin zaben a matsayin babban gwaji na dorewar kasar dake nahiyar Afirka ta Yamma tun bayan da rikici ya haifar da yakin basasa shekaru goma da suka gabata.

'Yan adawa na cewa matakin ya sabawa kundin tsarin mulki kasar amma ya ce hakan bai sabawa doka ba.

Amma me ya sa Mr Outtara zai sake tsayawa takara?

Ouattara ya shafe kusan shekaru 10 yana jan ragamar kasar ta Ivory Coast, kuma a cikin watan Maris din bana ya bayyana cewa ba zai nemi ta-zarce ba.

Amma abubuwan sun sauya daga watan Yuli saboda mutumin da Ouattara yake son ya gaje shi a matsayin shugaban Ivory Coast watau Amadou Gon Coulibaly - wanda shi ne firaiministan kasar, ya rasu sakamakon bugun zuciya ana tsaka da taron majalisar ministocin kasar a watan da ya wuce.

Shin wanene Alassane Ouattara ?

Alassane Ouattara ya zama shugaban kasar Ivory Coast ne a ranar 4 ga watan Disambar 2010 inda ya maye gurbin Laurent Gbagbo sannan a shekara ta 2015 aka sake zabensa domin wa'adin mulki a karo na biyu.

An haifi Alassane Dramane Ouattara a ranar 1 ga watan Junairun 1942 a garin Dimbokro kuma dangin mahaifinsa musulmai ne 'yan Burkina Faso masu rike da sarautar gargajiya kuma a a shekarar 1972 ya samu shaidar digirin digirgir daga jami'ar Pennslvania ta Amurka.

Kasancewarsa masanin tattalin arziki, ya yi aiki a wurare da dama ciki da hadda hukumar bada lamuni ta duniya - IMF da kuma babban bankin kasar.

Ya rike mukamin Firaiministan kasar daga shekarar 1990 zuwa 1993 kafin ya zama shugaban jam'iyyar Rally of the Republicans (RDR) mai mulkin kasar a shekarar 1999.

A bangaren iyali kuwa a shekarar 1991, Shugaba Alassane Ouattara ya auri bafaranshiya Dominique Nouvian, kuma suna da 'yaya biyu.