Yadda matan karkara ke fadi tashin ciyar da kansu da ma iyalinsu a Najeriya
Mata a yankunan karkara na ba da gagarumar gudunmowa a fagen noma da wadata al'umma da abinci da kula da yara har ma da alkinta ƙasa da ma'adanai.
Su ne a gaba-gaba wajen kai ɗauki a lokacin annoba kamar korona, duk da ƙaruwar ayyukansu na rainon 'ya'ya da ɗawainiyar gida a lokacin kulle.
Don tunawa da ɗumbin gudunmawarsu wajen ci gaban al'umma ne, Majalisar Ɗinkin Duniya ta keɓe duk rana irin ta yau 15 ga watan Oktoba, a matsayin Ranar Matan Karkara ta Duniya.
Taken bikin na bana shi ne "ƙarfafa wa matan karkara gwiwa a daidai lokacin da ake fama da annobar korona''.
Manufar hakan ita ce jan hankulan mutane da gwamnatoci game da halin matsin da matan karkara suke ciki, duk da irin gudunmawar da suke bayarwa.
Mata da 'yan mata sune aka bayyana sun fi shiga halin matsi tun bayan da duniya ta fada cikin annobar cutar Corona.
Tuni dama suka saba fadi tashi da habartu a cikin harkokin rayuwarsu ta yau da kullum a fannonin noma, kiwo da kula da iyali.

Malama Habi da ke wani kauye a jihar Jigawa ta shaida wa BBC irin yadda suke fafutukar gudanar da wasu kananan sana'oi don dagaro da kansu.
Ta ce,"Yanzu haka muna yin kamar kuli-kuli da daddawa da kuma rama, mu kan je jeji mu samo kamar ramar sai mu dawo gida mu dafa mu saka kuli-kuli, sannan mu dauka mu tafi talla".
Malama Habi ta ce idan suka yi sa'a suka je gidan masu hannu da shuni a kan musu kyautar kayan abinci a wani lokacin.

Ita ma Malama Hajara da ke kauyen Majiya a jihar Kano, ta shaida wa BBC cewa ta kan yi tafiya mai nisan gaske daga kauyen na su zuwa cikin birni domin yin aikatau don samun abin rufin asiri ita da 'ya'yanta da kuma maigidanta.
Ta ce,"Wanke-wanke nake zuwa ko kuma nayi wankau a gidajen mutane, a wani lokaci ma a kan kwashe wata biyu ba a biya ni ba sai daga baya sai a hada a bani shi yasa a wani lokaci na kan shiga gidajen mutane na samu dan dakan kayan miya na taya masu gidan ta yadda zan dan samu abin da zan mana cefane a ranar".
Malama Hajara ta ce,"A da nayi aikin birkila to sai na gamu da ciwon kirji sai na daina, ta ce zamu je asibiti amma a wani lokaci idan an rubuta mana magani bama iya siya, ga rashin ruwa, don wajen da muke zuwa iban ruwan akwai nisa a haka muke zuwa mu debo, ni banyi karatu ba, amma yarana shida duk sun yi".
Duk da ci gaban da mahukuntan ke cewa an samu wajen raguwar matsanancin talauci a fadin duniya, mutane kusan biliyan daya ne in ji Majalisar Dinkin Duniya ke ci gaba da fama da halin matsin tattalin arziki da bai kamata ba.
Sannan kuma sun fi yawa a yankunan karkara musamman a kasashe masu tasowa kamar Najeriya da har yanzu mata mazauna karkara ke cikin tsaka mai wuya, duk da cewa an samu ci gaba a wasu tsare-tsaren gwamnatocin jihohi na inganta rayuwar mutanen karkarar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta gano cewa yanzu mata su ne suka fi yawa wajen kawo habbakar tattalin arziki ta hanyoyin ayyukan kwadago da kananan sana'oi na cikin gida da waje.
Rashin cin gajiyar al'amuran more rayuwa da suka hada da kiwon lafiya da tsaftataccen ruwan sha da ilmin boko, matsaloli ne da har yanzu mata a karkara ake fama da su.
Sana'oi da sauran ayyukan da matan karkara kan gudanar don kyautata rayuwar iyali, na matukar taimakawa wajen rage fatara da ja'ibar yunwa har ma da samar da abinci a kasa.
To amma duk da hakan bai hana musu zama koma baya wajen cin gajiyar ababan more rayuwa daga gwamnatocin nasu.












