Zaɓen Amurka Na 2020: Trump ya koma kamfe a Florida duk da babu tabbacin ya warke daga coronavirus
Shugaba Donald Trump ya sake koma wa fagen yakin neman zabe, ƙasa da makonni biyu bayan da sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ya kamu da cutar korona.
Ya shaida wa dubban magoya bayansa, da akasari ba sa sanye da takunkumin fuska, cewa yana iya yi musu ''babbar sumbata'', a taron gangamin a kuma fagen faman yaƙin neman zaɓen jihar Florida.
Yayin da yake magana a Ohio abokin karawarsa, Joe Biden, ya zargi shugaban kan yin ganganci, tun bayan da aka tabbatar ya kamu da kwayarcutar.
'Yan takarar shugabancin kasar biyu na ta hanƙoron samun ƙuri'u yayin da makonni uku suka rage zuwa zaɓen 3 ga watan Nuwambar.
Kuri'un jin ra'ayoyin jama'a sun nuna cewa Mr Biden na kan gaba da Mr Trump da kashi 10.
Amma kuma, a jihar Florida, tazarar ba ta taka kara ta karya ba - inda jam'iyyar Democrat ke kan gaba da kashi 3.7, kamar yadda madaidaitan kuri'un da kungiyar Real Clera Politics ta tattara.
Fagen fafatawa kamar jihohin Florida da Ohio na da matuƙar muhimmanci wajen tattara ƙuri'u 270 na masu zaɓen shugaban kasa na musamman da ake bukata wajen cin galabar samun Fadar White House.
Mr Trump ya kamu da cutar korona kawanaki 11 da suka gabata, inda bayan kwana guda aka kwantar da shi a cibiyar kiwon lafiya ta Walter Reed.
Amma kuma a ranar Lahadi, wani likitansa ya bayyana cewa ba ya cikin hadarin yaɗa cutar ga sauran jama'a, kana a ranar Litinin ya bayyana cewa gwajin baya-baya da aka yi masa ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar a ciikin wasu 'yan kwanaki, duk da dai bai bayyana takamaimen kwanan watan ba.

Magoya bayan Trump sun fito don yin tozali da gwaninsu
A dandalin - daga Nomia Iqbal, BBC News, Sanford, Florida
An rika jin rerawar da aka saba ta ''Karin wasu shekaru hudu'' yayin da ɗaruruwa suka hau kan dogon layi suna shiga wani makeken filin saukar jiragen sama inda shugaban ya bayyana.
Ana ta yi wa mutane gwajin zafin jiki tare ba miƙa musu takunkumin sanyawa a fuska. Wadanda suka rufe fuskokin ba sa ganin cewa ya yi wuri shugaban kasar ya fito cikin jama'a.
Sun ce suna jinjina masa game da hakan. Mutum guda a nan ya shaida min cewa shi dan asalin birnin New York ne amma kuma ya mayar da jihar Florida tamkar gidansa - kamar dai ''gwaninsa'' Donald Trump.
Tawagar yaƙin neman zaɓen Trump na fafutuka tuƙuru a jihar ta Florida - faɗuwa zaɓe a nan ka iya haramta masa sake komawa Fadar White House.

Me Trump ya bayyana a gangamin?
A bayyanarsa ta farko bayan da aka gano yana ɗauke da cutar korona, Mr Trump mai cike da kuzari, ya sake dawowa kan salon yaƙin neman zaɓensa na sukar lamirin Mr Biden.
Ya yi tutiya da bunƙasar kasuwar hannayen jari, kafa dakarun hukumar sararin samaniyar Amurka da kuma nasarar tabbatar da alƙalan Kotun Ƙolin ƙasar - da na ukunsu Mai Shari'a Amy Coney da aka gabatar da sunansa a zauren majalisar dattawan kasar cikin wannan makon- a matsayin wasu manyan ayyukan ci gaba.
A gaban dubban jama'a, ya nisanta kansa da batun ƙara tsawaita dokar kulle da 'yan jam'iyyar Democrat ke goyon baya tare da dasa ayar tambaya game da yanayin zurfin tunanin Mr Biden.

Asalin hoton, Reuters
Yayin da yake danganta batun warkewarsa daga cutar korona, ya ce: ''Sun ce ina da garkuwa - na ƙara jin wani karfi. Zan iya takawa daga nan in sumbaci kowa. Zan sumbaci maza da kuma kyawawan mata, zan muku wata wawiyar sumbata.''
Mutane kalilan ne ke sanye da takunkumin rufe fuska, ko kuma kiyaye dokokin kiwon lafiya na bayar da tazarar akalla taku shida tsakanin juna don rage hadarin yaduwar cutar korona
Me yasa jihar Florida ke da muhimmanci ?
Ba abin mamaki ba ne cewa jihar Florida - da ke yi wa kirarin ''Hasken rana'' - nan ne inda Trump ya gudanar da gagarumin gangamin yaƙin neman zaɓensa.
Ya so da kuma buƙatar lashe zaɓe a Florida, jihar da ya sha da ƙyar a zaben shekara ta 2016. Nan ma gidansa ne. Dan asalin birnin New York, a watan Satumbar bara ne kuma ya mayar da kansa dan asalin jihar Florida.
Yin dab-da-dab a fafatawar a jihohi masu muhimmanci na nufin zai iya samun galabar sake cin zaben wajen lashe kuri'un manyan mazaɓu a yankuna masu tasiri.
Jihar Florida na daga cikin jihohi shida da ke da yawan ƙuri'un manyan mazaɓu - 29 cikin jimullar ƙuri'u 538 na ake buƙatar lashewa.











