Shin Wizkid ya yi wa Buhari raini ne a Twitter?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ana cacar baki da musayar kalamai a shafin Twitter tsakanin shahararren mawaƙin Najeriyar nan Wizkid da kuma mai ba wa Shugaba Buhari shawara kan kafofin sada zumunta Lauretta Onochie.

Tun da farko, Shugaba Buhari ne ya aika wa Shugaban Amurka Donald Trump saƙon jaje a shafin Twitter sakamakon cutar korona da ta kama Mista Trump ɗin.

Wannan lamari ne ya fusata mawaƙin na Najeriya wato Wizkid inda ya ce Shugaba Buharin bai da wani haɗi da Donald Trump, haka kuma ya zargi 'yan sanda da rundunar SARS da kashe 'yan Najeriya a kullum.

A martanin na Wizkid dai, ya kira Shugaba Buhari "Tsohon Mutum" ya kuma gargaɗi shugaban da cewa ba shi da haɗi da Amurka kuma ya mayar da hankali kan ƙasarsa.

Waɗannan kalaman na Wizkid ne suka fusata mai bai wa Buhari shawara kan kafafen sada zumunta Lauretta Onochie inda ta ce ba wai raini ba ne mutum ya kira wani tsoho ba, amma yadda Ayo Balogun wato Wizkid ya kira shugaban "Tsohon Mutum", abin ya yi nauyi a baki.

Lauretta Onochie ta ce Wizkid na tattare da ''jahilici da yarinta''.

A martanin farko da ta mayar masa, ta kuma ce a yanzu sunansa na waƙa ya tashi daga Wizkid zuwa Dumbkid, ma'ana "daƙiƙin yaro".

Bayan wannan martanin ne shi kuma Wizkid ya sake mayar da martaninsa na biyu inda ya yi dariya ya ce: "Mutum mai shekara 77 ba yaro ba ne. Ke mace ce kuma uwa ce, haka kuma 'yan sanda da rundunar SARS na kashe yara, abin da za ki iya cewa kenan? kin ji kunya! ni uba ne kuma mahaifi ne, babu batun shekaru da neman shugabanci nagari a ƙasata!"

Me 'yan Najeriya ke cewa?

Tun da aka fara cacar baki tsakanin mutanen biyu a shafin Twitter su ma jama'a suka fara mayar da martani da ra'ayoyinsu kan musayar kalaman da ake yi tsakanin Wizkid da Lauretta.

Wannan mai suna Jamilu cewa ya yi wannan yaron ya mayar da hankali kan waƙarsa. A cewar Jamilu, shi ba mai goyon bayan Buhari bane amma yana ƙalubalantar Wizkid me ya sani a kan gudanar da aikin gwamnati?

Wannan kuma cewa ya yi hakan na daga cikin dalilan da ya sa na tsani wannan yaron Wizkid saboda tsananin rashin kunyarsa. Ya gargaɗe shi da cewa zai iya sayar da waƙoƙinsa ba sai ya bi ta wannan hanyar ba.

Wannan goyon bayan Wizkid yake yi inda ya ce mawaƙin ba wai ƙalubalantar shugaban ƙasar yake yi ba, saƙo kawai ya wallafa.

Ya ce Wizkid na daga cikin muryoyin Najeriya kamar mawaƙi Eidris Abdulkarim, a cewarsa, idan duka mawaƙa za su haɗa kansu za su iya kawo ci gaba a Najeriya.

Wannan kuma ya saka wa mawaƙin albarka inda ya buƙaci mawaƙin ya nuna wa sauran mawaƙa irin wannan hayar. Ya kuma ce abin da ya faɗi yana da amfani kuma yana amfani da damarsa yadda ya kamata.