Kalli bidiyon ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi a jihar Jigawa
An wallafa
Al'ummomi da dama ne ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Nigeria, inda aka samu asarar rayuka da ta dukiyoyi.
Fiye da mutum 40 ne suka mutu a ambaliyar ruwan sannan dubban gidaje suka rushe, aka kuma yi asarar amfanin gona na miliyoyin Naira.
Hukumomi a jihar ta Jigawa sun ce fiye da mutum 10,000 ne suka samun mafaka a sansanoni 30 da aka samar musu.
Wannan ce mafi munin ambaliyar ruwa da aka fuskanta a jihar Jigawa cikin shekaru da dama.








