Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hukumomi a Ghana sun lashi takobin murkushe shirin 'yan aware
Jami'ai a yankin Volta dake kasar Ghana sun lashi takobin murkushe duk wani yunkuri da 'yan awaren kasar ke yi na tada zaune tsaye.
Gargadin na zuwa ne kasa da awanni 48, bayan da mayakan kungiyar 'yan awaren da ke neman ballewa daga kasar don kafa tasu kasar.
'Yan sanda da sojoji sun ce an kashe wani dan kungiyar 'yan awaren yayin da aka kama fiye da talatin.
An ba da rahoton cewa wani kwamandan 'yan sanda ya samu rauni yayin harin.
Kungiyar ta kwashe sama da shekaru goma tana yakin neman kafa sabuwar kasar da ake kira Western Togoland.
An kame mutane da yawa a shekarar da ta gabata, amma an yi watsi da tuhumar cin amanar da aka yi musu.
Har yanzu dai ba a sani ba ko tashin hankalin na ranar Juma'a na da nasaba da zabuka masu zuwa a Ghana ba.
Yayin harin na ranar Jumma'a, wasu rahotanni sun ce an kashe karin wasu jami'ai uku, tare da tserewa da wasu uku.
Ministan yankin Archibald Letsa, ya ce an kai harin ne da hantsi a garuruwan Aveyime da Mepe a yankin Volta.
"Muna aiki don ganin an saki' yan sandan, mun tsinci kanmu cikin damuwa saboda wannan al'amari'' In ji shi.
Ya ce 'yan awaren wadanda ke son kafa sabuwar kasa sun kafa shingaye a wurare daban-daban na shiga yankin, mai nisan kilomita 150 daga arewa maso gabashin Accra babban birnin kasar.