Yajin aiki: Ƙungiyar Kwadagon Najeriya ta ce ba gudu, ba ja da baya

An wallafa

Babbar Ƙungiyar Kwadago a Najeriya NLC ta ce ba gudu ba ja da baya a shirinta na fara yajin aikin gama gari.

Ƙungiyar ƙwadagon ta ce sun tashi baram-baram daga tarukan da suka yi da gwamnatin tarayya marecen jiya Alhamis, don haka tana nan a kan ƙudurinta na tafiya yajin aiki daga ranar Litinin.

Ta ce tarukan sun gaza wajen biyan buƙatun da suka gabatarwa gwamnati, don haka yajin aikinsu ba gudu ba ja da baya.

Kwamared Nasir Kabir, shi ne mataimakin sakataren ƙungiyar NLC, kuma ya yi gaya wa Mukhtari Adamu Bawa halin da ake ciki:

"Kungiyar Kwadago kamar yadda 'yan Najeriya suka sani, wannan taro da muka yi da bangaren gwamnati babu abin da aka cimma kuma mun tashi ne baram-baram. Ina mai tabbatar wa 'yan Najeriya cewa yajin aiki da muka kira, in sha Allahu da wa'adin nan ya cika wato ranar Litinin, za mu tashi da gagarumin yajin aiki a Najeriya. za a tsunduma cikin yajin aiki."

Idan ba a manta ba, gwamnonin wasu jihohin Najeriya sun shiga tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadagon domin sasanta su. Sai dai da alama hakan bai samu ba.

Kwamared Kabir: "Mu shawarar da muka kawo ita ce a duba halin da 'yan Najeriya ke ciki. Babu gwamnatin da za ta ga talaka yana cikin wannan mawuyacin halin ta kuma ce za ta yi kari kan ttsadar rayuwarsa".

A kan hasken lantarki, Kwamared Kabir ya ce har yanzu lantarki bai ishi masu bukatarsa a cikin kasar ba.

A nata bangaren, gwamnatin Najeriya ta ce tayi ƙare-ƙaren kudaden man fetur da na hasken lantrki ne saboda ta inganta ko bunkasa kudaden shigar da ta ke samu. Ta kuma bayyana cewa za ta yi amfani da kudaden wajen aiwatar da ayyukan raya kasa ne.

Sai dai kungiyar kwadagon ta ce wannan ba dalili ne da zai gamsar da ita ba.

"Sau nawa wannan gwamnatin ke kara farashin man fetur? Duk lokacin da ta yi kari sai ta ce ta janye tallafi ne, kuma mun sha tambaya wai shin tallafin nan haihuwa yake yi ne?"