Super Cup: Bayern Munich 2-1 Sevilla - Javi Martinez ya taka rawar gani

An wallafa

Wankin hula ya so ya kai Bayern Munich ga dare a fafatawar da ƙungiyar ta yi da Sevilla ta Sfaniya a birnin Budapest amma ta nuna bajinta da juriyar da ta ba ta nasara a gasar UEFA Super Cup ta 2020 wanda ya ba ta damar haɗa kan kofi huɗu ke nan a wannan shekarar kawai.

A wannan karon an gayyaci 'yan wasa 15,180 domin su kalli wasan a Puskas Arena, kuma wannan ne babar gasar ta farko a Turai da aka kyale 'yan kallo su halarta tun da annobar korona ta tilasta akakulle filayen wasa.

Sai da Bayern ta jajirce kafin ta sami wannan nasarar, domin Sevilla ce ta fara shiga gaba bayan da ta zura kwallo a ragar Bayern ɗin a minti na 13 yayin da Lucas ocampos ya dauki bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da David Alaba ya kayar da Ivan Rakitic.

Amma Bayern ta farke kwallon kafin a tafi hutun rabin lokaci, inda Leon Goretzka ya zura wata kwallo da ta burge 'yan kallo bayan da Robert Lewandowski ya gyarota.

Bayan da aka dawo hutun rabin lokaci kowace kungiya ta yi kokarin sake zura wasu kwallayen. Misali 'yan wasan Bayern Lewandowski da Leroy Sane sun ci kwallo biyu amma alkalin wasan ya hana.

Bayern ta lashe gasar ne a minti na 104 bayan da Javi Martinez ya buga kwallon da kansa yayin da Bayern ta kai wata kora ta hannun Alaba wanda gola SEvilla Yassine Bounou ya kasa kamawa.

Bayern sai san barka a bana

Wannan wasan shi ne wasa na 32 da Bayern Munich ta buga a jere ba tare da an doke ta ba a dukkan gasar da ta buga, kuma nasarar da ta samu ce ta kawo ƙarshen jerin wasanni 21 da sevilla ta ɗauka ba a sami wanda zai buge ta ba.

Abin da yafi jan hankalin jama'a shi ne yadda aka bar 'yan kallo suka kalli wasan duk da yake sun zarce 15,000 ne a filin wasan Puskas Arena da ka iya ɗaukar 'yan kallo 67,000.

Sai dai duk da wannan, abin da ya fi fitowa fili shi ne Bayern Munich ce Zakarar Turai a kowane matakin da aka duba.