Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Water Resources Bill: Me ya sa ƙudurin dokar ruwa ta Najeriya ya jawo ce-ce-ku-ce?
Gwamnatin Najeriya ta soma gabatar da ƙudirin dokar albarkatun ruwa mai suna National Water Resources Bill ne a 2018 lokacin majalisar dokoki ta Takwas.
Majalisar wakilan ƙasar ta amince da ƙudurin dokar amma tawakararta ta dattawa ta yi watsi da ita bayan da Sanata Godswill Akpabio, lokacin yana kan muƙamin shugaban marasa rinjaye ya jagoranci ƴan hamayya wajen yin fatali da shi.
Shugaban majalisar dattawa na wancan lokacin Sanata Bukola Saraki, ya buƙaci su koma da shi wurin ɓangaren zartarwa domin su gyara shi kafin su sake dawo musu da shi, amma hakan bai faru ba har wa'adin mulkinsu ya ƙare.
A watan Yulin 2020 ne gwamnati ta sake komawa da ƙudurin dokar ga majalisar dokoki ta Tara, kuma hakan ya sa wasu 'yan Najeriya sun riƙa sukarsa.
Wasu daga cikin fitattun mutanen da suka bayyana adawarsu ga kudurin dokar sun haɗa da shahararren marubucin nan Farfesa Wole Soyinka, gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, Kungiyar Kwadago ta Najeriya, ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere, da sauran irinsu.
Sun yi zargin cewa idan aka zartar da ƙudurin dokar za ta raba kawunan 'yan kasar.
Sai dai gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ƙudurin dokar ruwa ba wani sabon abu ba ne tana mai cewa ta ɗan yi ƙare-ƙare a kansa ne domin ya dace da tsarin ƙasashen duniya.
Mene ne ƙudurin dokar ruwa ta Najeriya2020?
Gwamnati ta haɗe wasu dokokin albarkatun ruwa huɗu da dama da ake da su, sai suka haɗu suka zama ƙudurin dokar National Water Resources Bill ta shekarar 2020.
- Dokar Albarkatun Ruwa ta Cap W2 LFN 2004
- Dokar Hukumar Kula da Kogunan Najeriya RBDA ta Cap R9 LFN 2004
- Dokar Hukumar Kula da Albarkatun Ruwa ta Cap N1100A, LFN 2004
- Dokar Cibiyar Albarkatun Ruwa ta Ƙasa ta Cap N83 LFN 2004
Ƙudurin dokar albarkatun ruwan na son dukkan abin da ya shafi iko da albarkatun ruwa na dandaryar ƙasa da na ƙarƙashin ƙasa da na koguna su kasance ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya.
A cewar Ministan Yaɗa Labarai da Al'adu Lai Mohammed ne ya tsara ƙudurin don samar da ƙwararrun ma'aikata kan kula da ruwan dandaryar ƙasa da na ƙarƙashin ƙasa da zai amfani ƴan Najeriya.
Ya ƙara da cewa gwamnati ba ta da wani ɓoyayyen ƙuduri kan hakan sai don ci gaban ƙasa.
Me ya sa ƙudurin dokar ya harzuƙa wasu mutanen?
- Sashe na 98
Wannan sashen na ƙudurin dokar ya ce ''amfani da ruwa zai dogara ne kan samun lasisi''. Hakan na nufin cewa kafin kowa ya fara wani aiki na ruwa, dole ya samu lasisi daga wajen hukumar gwamnati da ke da alhakin hakan.
- Sashe na 104: Ikon gaggawa idan ana rashin ruwa
Wannan dokar za ta bai wa gwamnati ikon rage yawan ruwan duk mutumin da ke amfani da ruwan da ya fi ƙarfin wanda suke buƙata shi da iyalinsa, don samun iya wanda zai ishe su kawai.
- Sashe na 107: Gwamnati na da ƙarfin ikon soke lasisinka
Dokar na iya soke lasisin duk wanda ke ɓarnar ruwa.
- Sashen na 120: Dole ƴan Najeriya su samu izini kafin su tona burtsatse
Ba wata ƙungiya ko wani mutum da za su iya tona burtsatse a ko ina a Najeriya idan har ba su samu takardar izinin yin hakan ba daga hukumar.
- Sashe na 125: Zuwa duba yadda ake amfani da ruwa
Sai ma'aikatan hukumar ne kawai za su iya dinga zuwa duba yadda ake amfani da ruwa akai-akai ko yadda ake kai ruwa wurare, kuma dole su dinga tafiya da katin shaidarsu idan hakan ta taso.
- Sashe na 131: Rashin bin doka
Babu wanda zai iya amfani da ruwa idan bai bi dokokin wannan ƙuduri ba.
Jihohi za su iya amfani tare da yin iko ne da albarkatun ruwan da ke faɗin jihohinsu kawai, kuma za su yi amfani ne da tsari da dokokin da gwamnatin tarayya ta samar.
Ba a taɓa samun wata doka ta amfani da ruwa da za ta amfani mutane sosai ba.
Yadda mutane suka ji da dokar
Gwamnan Binuwai Samuel Ortom ya ce matakan da ke ƙunshe a ƙudurin dokar Albarkatun Ruwa Ta Ƙasa ta 2020 ba su yi daidai da abin da Dokar Amfani da Fili ta faɗa ba, yana mai cewa gwamnati tana da wani ɓoyayyen ƙuduri.
Farfesa Wole Soyinka ma a wata sanarwar da ya fitar a watan Agustan 2020, ya yi gargaɗin cewa idan aka amince da ƙudurin dokar, zai bai wa shugaban ƙasa cikakkiyar dama ce ta yin iko da dukkan albarkatun ruwa na dandaryar ƙasa da na ƙarƙashin ƙasa.
Wasu ƙungiyoin ma da dama sun soki ƙudurin dokar.
Amma duk da haka akwai masu yabon wannan ƙudurin.
Kwamred Adeniji ya wallafa a shafin Tuwita cewa: ''Yanzu ku lura duk masu kushe Ƙudurin Dokar Albarkatun Ruwa ta Ƙasa ta 2020 ba su karanta tare da fahimtar abin da ta ƙunsa ba. #WaterBill2020''
Abin da gwamnati ta ce
Ministan Yaɗa Labarai da Al'adu Lai Mohammed da Ministan Albarkatun Ruwa Injiya Suleiman Adamu sun yi bayani kan ƙudurin dokar ruwan ta 2020 a wajen wani taron manema labarai ranar 21 ga watan Satumban 2020.
Mista Lai ya ce masu sukar ƙudurin dokar ba su ma nutsu sun karanta abin da ta ƙunsa ba, kawai suna karanta abin da mutane ke faɗa ne.