Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana neman fursunonin da suka yi tsirara suka tsere daga gidan yari a Uganda
Hukumomi a Uganda sun bayyana cewa an kama fursunoni bakwai cikin 219 da suka tsere daga wani gidan yari da ke arewa maso gabashin ƙasar.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin fursunonin sun tuɓe ruwan ɗorowar kayan fursunan da suke sanye da su, inda suka gudu tsirara cikin tsaunuka domin kada a gane su.
Ana tunanin fursunonin na ƙoƙarin amfani da tsaunuka domin ratsawa cikin ƙasar Kenya.
Fursunonin sun kashe wani soja a lokacin da suka tsere daga gidan yarin da ke a garin Moroto a ranar Laraba.
Mai magana da yawun sojojin ƙasar ya bayyana cewa an kashe mutum biyu cikin waɗanda suka tsere.
Jami'an sojin ƙasar da gandirebobi na ci gaba da neman waɗanda suka tseren, inda ake zargi sun gudu da bindigogi 15.
Gidan yarin, wanda yake da aƙalla fursunoni 600, an gina shi ne kan wani tsauni a garin Moroto, kuma a kusurwar garin.
Tuni dai aka rufe gidan yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan yadda lamarin ya faru.
Rahotanni a ranar Laraba sun bayyana cewa harbe-harben da aka yi sun sa kasuwanci ya tsaya cik a yankin.
Moroto shi ne gari mafi girma a yankin Karamoja, yankin da ke da akwai makiyaya da dama kuma ya shahara wurin yaƙi da bindiga, kamar yadda wakiliyar BBC Patience Atuhaire daga Kampala ta shaida.
Wani shiri da gwamnatin ƙasar ta yi a shekarar 2000, ta yi ƙoƙari ta karɓe bindigogin da ke hannun farar hula, amma an ci gaba da samun arangama tsakanin al'ummomi a yankin.