Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kullen coronavirus: An ƙirƙiri manhajar sauƙaƙa wa mutane sayen kwaroron roba a Uganda
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Matakin kulle daka sanya don hana yaɗuwar cutar korona a Uganda ya hana mutane samun damar sayen magungunan tsarin iyali da suka haɗa da kwaroron roba.
Sai dai wata manhaja ta Safe Boda da mutane ke iya odar kayayyaki kuma a aika musu har gida ta sauƙaƙa wa mutane tare da ba su damar sayen kwaroron robar da dama yawanci a kan ji kunyar saya ido na gani ido, kuma akai musu har gida.
Sannan su ma masu kai saƙon manhajar ta zame musu alkairin wajen ƙara samun ciniki.