Me ya sa mutane ke yin shafe-shafe don sauya launin fatarsu?

    • Marubuci, Daga Brishti Basu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • An wallafa

Bambancin launin fata wani salon nuna wariya ne da darajar wadanda fatarsu ke da haske tsakanin rukunin al'umma. Duk da illar yin haka a cikin al'ummar sassan duniya, ba a fiya tsokaci kan batun ba - sai a yanzu.

A karon farko mazauniyar New Zealand Harsharin Kaur ta ziyarci India, kasar kakaninta, ta kaɗu da matsin da ta fuskanci ana yi wa mutane na sauya launin fatarsu a ƙasar.

Allunan fina-finai na nuna alamomin cewa sai wadanda launin fatarsu ke da haske a mata da maza ne kawai za su iya samun shiga a masana'antar fina-finai. Tallan talabijin kan kayayyakin gyaran jiki na jaddada cewa yanayin haske jikin mace na da tasiri kan damar da take da ita ta samun aiki, miji ko farin ciki.

"Garnier da L'Oreal - kamfanonin da ban taɓa ganin suna tallata irin wadannan kayayyakin ba a New Zealand. Amma a India, talla abubuwan da ake ta yi kenan," a cewar Kaur, wanda ke da fitaccen shafin Instagram na The Indian Feminist.

A Yuni 2020, lokacin da yake tsaka da fuskantar suka, L'Oreal ya sanar da cewa zai cire kalmar "white, wato "fari', "fairness", wato "haske" da "light" shi ma "haske" daga dukkanin kayayyakinsa - musamman a mayukansa na Garnier, wanda ake tallatawa a matsayin man sa farin fata a akasarin ƙasashen kudancin Asia.

Duk wadannan ƙasashen da al'ummarsu da dama ke da fata mai duhu - akwai mayukan da ake kai musu na sauya launin fata da wanda ke kare su daga kunar rana.

Wariya da bambancin launin fata

Nuna bambanci launin fata tsakanin mutanen da suka fito daga ƙabila guda akwai takaici. Wannan kusan ita ce maganar da ake yawaita yi tsakanin bakar-fata, bambancin launin fata abu ne da ba a fiya magana a kai ba, duk da damuwa da jefa mutane cikin mugun hali ko kisa da yake haifarwa.

Amma kisan George Floyd a Mayu 2020, da ya haifar da zanga-zanga da ce-ce-ku-ce kan wariya ko nuna ƙyama, ya ankarar da mutane da kasashen kudancin Asia da mazauna ƙetare.

Wani sabon shirin Netflix mai suna "Indian Matchmaking" ya haifar da muhawara da ka-ce-na-ce bayan jagoran shirin, tana nuna wariyar launin fata tsakanin masu shiga shirin.

A lokacin wannan zanga-zanga da ci gaba da nuna ko fito da batutuwan da suka shafi wariya har a al'adu, mutane da dama na sake nuna takaici da alla-wadai da nuna bambanci kala da mayukan da ake yi don sauya fata.

'Fari & abin so'

Wasu kamfanonin sun mayar da martani. Unilever, kamfanin mayukan kara hasken fata na Fair & Lovely, ya sanar da cewa duk mayukan gyaran fata da yake yi za su kasance dauke da kalmomi sauya hasken fata kamar "fairness", "whitening", and "lightening" za a cire su, sannan man zai sauya suna daga Fair & Lovely zuwa Glow & Lovely.

Kakakin kamfanin ya ce wannan sauyi da za a yi wa mayukan na kan hanya, sai dai ana kara matsa musu - da bukatar su kaddamar da gangamin janye mayukan baki daya daga kasuwa, sannan mutane a shafukan sada zumunta na alla-wadai da shugaban kamfanin Unilever Alan Jope ya kalamar suka da wariya da cigaba da sayar da man da ke sama musu ribar £256m-a-shekara.

Yayinda sauyin sunan zuwa Glow & Lovely ya janyo mutane ke ta yabawa kamfani, kwararu na cewa bai wadatar ba. Saboda har yanzu ana ganin wadanan mayukan a shaguna.

Suka da kalmar "Glow"

"Ban sani ba ko akwai wani bambanci. Na yaba musu saboda man su na daya daga cikin wanda ya yi fice. Amma nayi takacin jin cewa sunan zai koma 'Glow & Lovely' saboda kalmar Glow kamar sake maimaita 'lightening'," ma'ana farar fata a vrwat Nikki Khanna, farfesa a jami'ar Vermont wacce ta jima tana karatu akan alakar jinsu da launin fata sama da shekara 20.

"Kalmar 'glow' ita kanta - abin da take nufi da tallan da take yi shekaru da dama [kan mata] na nufin farar fata. Fatan shi ne ana sake inganta hakan - kuma ina nace 'ingantawa' abin da nake nufi shi ne kawar da man."

Illar nuna bambancin launi fata

Yayinda ake ganin akwai bukatar sake bincike, nazarce-nazarce da dama sun nuna illar da bambanci launin ke haifarwa.

Daya daga cikin illar ita ce matsalar ƙwaƙwalwa. Wani bincike, misali ya nuna matsaloli da alamomin damuwa da tsangwama da ake nunawa masu fakar fata tsakanin mata Amurka asalin Asiya.

"A tarihi, mutane da dama sun na ganin bakar fata a matsayin abu mara kyau, da raini ko rashin ilimi da ya jima yana yawo tsakanin al'umomi a ciki da waje." a cewar Alisia (Giac-Thao) Tran, daya daga cikin malamai da ke bincike a jami'ar Arizona.

"Tsakanin al'umomin kudancin Asiya, wannan tarihi ne da ya jima kan tsangwama da matsalolin fata."

Tallan hada aure

Wannan bincike ba abun mamaki ba ne. An fi mayar da hankali kan amare masu farar fata wajen hada su da maza a tallan da ake wallafawa a jaridu tsawon shekaru; ana nuna mata masu farar fata a talla a wani salo na janyo hankali maza masu bukatar mata.

Shafin na tambayar masu ra'ayi su bayyana irin kalar fatar da suke so kuma suna bai wa masu ra'ayi zabi da nau'ikan kalolin fatan da ake da su.

Sauya kalar fata 'Skin filters'

"Jaridu na amfani da kalar fata wajen talla da janyo hankali. Kamfanonin da ke aikata hakan, kamar yadda mutane ke yi, shekaru hudu zuwa biyar da suka gabata, mun yanke hukunci janye wa daga amfani da manhajar sauya fata wajen yin hadi," a cewar Adish Zaveri babbar jami'ar kasuwanci a Shaadi.com.

Da wani labarin ya isa ga wata kungiya a Facebook ta Mata Asia mazaunan arewacin Amurka, an kaddamar da korafi domin janyo hankali kan shafin shaadi.com.

"Cikin sa'o'i 24, mu samu mutane 1,500 da suka sanya hannu a gangamin." a cewar Hetal Lakhani mazauniyar Dallas ta Texas da ta kirkiri korafin.

Sauyin al'adu

Yayinda bambancin launin fata ya kasance abin da b aa taba tankawa ba a kudancin Asiya har sai zuwa wannan lokaci, shafukan sada zumunta da intanet sun taka rawa wajen sauya wannan tunani.

Wani littafi da wata mata ruwa biyu, Khanna ta rubuta kwanan nan mai taken: Asian American Women on Skin Color and Colorism ya yi nazari kan tasiri da halin da mata suka shiga daga yankunan daban-daban da yanzu haka ke zama a Amurka

Basirar da ta samu a bincike rubuta littafin, ta ce, misali ne mai kyau kan yadda intanet ke sauya tunani da tattauna batutuwan da suka shafi nau'in fata.

Gangami a shafukan sada zumunta

Khanna ta soma wannan shirin a 2017 da bukatar mika korafi a Facebook. "Shafukan sada zumutan ya tana muhimmiyar rawa wajen taimaka wajen samun bayanai daga mata da suka zarta wanda nake da su a shafina," a cewarta.

Khanna ta ce tayi mamaki da alkaluman mutane da suka nuna cewa basu da masaniya cewa bambancin launin fata babban batu ne tsakanin al'ummar Asiya da mazauna ketare.

Amma sannu a hankali, wannan tunanin ya kawar - godiya ga shafukan sada zumunta da gangamin da aka yi cewa Bakar-fata kala ce mai kyau kuma bakake kayawawa ne wanda aka rinka amfani da maudu'in #blackisbeautiful wajen ankarar da mutane.

Wannan maudu'in ya taimakawa bakaken fata fitowa su bayyana ra'ayoyi da tsokaci kan irin abubuwan da suka fuskanta, hakan ya karya wannan alkadarin da kushe da ake yiwa nau'in fata.

Taran ta yarda cewa kafar sada zumunta ko sociyal mediya na iya taka muhimmiyar rawa da tarwatsa duk wani tanunin baya da bai wa mutane damar bayyana ra'ayoyi. Akasarin wadanan mutane rukuni ne na masu tasowa da ke fahimtar gibin da ake da shi tsakanin wariya da bambancin launi. Maimakon su dauki karatun kokarinsu shi ne watsi da hakan.