Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Navid Afkari: Matashin ɗan kokowar da Iran ta kashe kan zargin kisan jami'in tsaro
Iran ta zartar da hukuncin kisa kan ɗan kokowar da aka zarga da aikata kisa, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.
Iran ta bijere wa kiraye-kirayen ƙasashen duniya da suka nemi a dakatar da zartar da hukuncin.
Navid Afkari, mai shekara 27, an yanke masa hukuncin kisa ne kan kisan wani jami'in tsaro a lokacin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a 2018.
Ya ce an tursasa masa amsa laifin ne ta hanyar azabtar da shi.
Ƙungiyar ƴan wasa mai wakilai 85,000 tana cikin waɗanda suka nemi a dakatar da zartar da hukuncin.
Ƙungiyar ƴan wasa ta duniya ta ce an yi masa "ƙazafi ne" saboda ya shiga zanga-zanga, inda ta yi kira da a kori Iran daga dukkanin harkokin wasanni idan har ta zartar da hukuncin.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi roƙon jin-ƙai ga ɗan kokowar inda ya ce "laifinsa kawai shi ne shiga zanga-zangar ƙin jinin gwamnati."
Hukumar shirya wasannin Olympics ta IOC ta bayyana hukuncin a matsayin "labari marar daɗin ji" inda ta jajanta wa iyalansa.
Iran ta zartar da hukuncin kisa ne kan Afkari ta hanyar rataya a birnin Shiraz da ke kudancin kasar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Haka kuma an yanke wa ƴan uwansa Vahid da Habib hukuncin ɗauri daga shekara 54 zuwa 27 a gidan yari, kamar yadda masu fafutikar kare haƙƙin ɗan Adam a Iran suka bayyana.
Wata murya da aka naɗa daga gidan yarin da aka tsare shi, Afkari ya ce an azabtar da shi. Mahaifiyarsa ta ce an tursasa wa ƴaƴanta ne su dora wa kansu laifin da ba su aikata ba.
Lauyan da ke kare su, Hassan Younesi, a Twitter ya ce saɓanin rahotanni daga Iran, babu bidiyo da ke nuna lokacin da aka kashe jami'in tsaron na Iran.
Ya ƙara da cewa an yi amfani da bidiyon ne domin kafa hujja a shari'ar bayan kuma an ɗauki bidiyon ne bayan sa'a ɗaya da al'amarin ya faru.
Hukumomin Iran sun musanta zargin sun azabtar da ɗan kokowar
Afkari zakara ne a fagen kokowa a ƙasar, wasan da ya shahara kuma ke da tarihi a Iran.