Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jamal Khashoggi: Saudiyya ta soke hukuncin kisan waɗanda suka kashe ɗan jaridar
Wata kotu a Saudiyya ta rage hukuncin kisan da aka yanke wa mutum biyar da aka samu da laifin kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi a 2018.
Masu shigar da ƙara sun ce an mayar da hukuncin zuwa zama kurkuku na shekara 20 bayan da iyalan mamacin suka yafe wa mutanen da suka hallaka ai gidan nasu.
Amma matar da yake shirin aura kafin aka kashe shi ta ce shari'ar "wasan yara ce."
An dai kashe Khashoggi ne a cikin ƙaramin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Santanbul , kuma mutanen da suka kashe shi jami'an gwamnatin Saudiyyar ne.
An kuma san shi da sukar lamirin gwamnatin ta Saudiyya.
Hukumomin ƙasar sun ce an kashe shi ne ba tare da saninsu ba, kuma bayan shekara guda ƙasar ta gurfanar da mutum 11 a gaban wata kotu tana tuhumarsu da aikata kisan.
Wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman ta yi watsi da shari'ar gabi ɗayanta. Shugabar hukumar Agnes Callamard ta bayyana cewa "Da gangar aka kashe Khashoggi kuma kisan na gilla ne."
Ms Callamard ta kuma ce akwai kwararan shaidu da suka tabbatar manyan jami'an gwamnati har da Yarima Mohammed bin Salman na da hannu dumu-dumu cikin kisan.
Yariman ya musanta aikata laifin amma wasu masu yi ma sa hidima su biyu na fuskantar shari'a a Turkiyya a bayan idonsu, akwai kuma wasu mutum 18 da Turkiyya ke tuhuma da aikata mummunan laifin.
Kafofin yada labarai mallakin gwamnatin Saudiyya sun bayyana wannan hukuncin a matsayin na karshe da ka yanke wa mutanen da aka samu da laifin kisan Jamal Khashoggi - tsohon dan jarida dan kasar ta Saudiyya da ya rika sukar lamirin yarima mai jiran gadon sarauta Mohamed bin Salman.
A farkon wannan shekarar iyalan gidan marigayi Khashoggi suka bayyana cewa sun yafe wa wadanda suka kashe mai gidan nasu, kuma sun ce sun yi amanna cewa ba da gangar aka kashe shi ba.
Wannan ne matakin da ya share fagen rage tsaurin hukuncin kisan da aka yanke wa mutanen da aka samu da aikata wannan mummunan laifin.