Coronavirus: Kusan mutum 3,000 sun kamu cikin awa 24 a Burtaniya

An wallafa

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa kusan mutun 2,988 ne suka kamu da cutar korona a kasar a cikin sa'a 24.

Kididdigar gwamnati ta nuna cewa wannan ne karon farko da aka samu irin wannan adadi tun bayan 22 ga watan Mayu.

Ministan lafiya Matt Hancock ya ce babban abin damuwa shine irin yadda cutar ta yawaita a tsakanin matasa.

A yanzu yawan wadanda annobar Korona ta yi ajalinsu a Burtaniya ya kai 41,551.

Mr Hancock ya kara da cewa yana da matukar muhimmanci al'umma su taka rawarsu wurin kokarin dakile annobar, ta hanyar kiyaye ba da tazara.

A cewarsa rashin kiyaye matakan kariyar zai iya sa a shafawa tsofaffi da ke zaune a gida, da dama sun fi kowa shiga hadari idan suka kamu.

Duk da haka Mr Hancock ya kare matakan gwamnati na bude makarantun firamare, lura da illar da rashin bude makarantun zai yi ga kananan yara.