Sharuddan da Najeriya ta gindaya wa jiragen kasashen duniya

FMAVIATIONNG

Asalin hoton, FMAVIATIONNG

Bayanan hoto, Wata hudu kenan da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya
An wallafa

Wata hudu bayan dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya, ministan sufurin jiragen sama na kasar Hadi Sirika ya sanar da wasu sharuddan dawo da zirga-zirgar jiragen kasa da kasa daga ranar Asabar.

Ministan ya ce an tabbatar da dawo da zirga-zirgar jiragen saman daga ranar Asabar ne bayan ma'aikatarsa ta tabbatar da kammala dukkanin wani shiri na kauce wa shiga hadari.

Kamar yadda gwamnatin ta sanar a baya, filayen jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja da na Murtala Muhammad da ke Legas ne za su fara budewa da jiragen kasashen waje.

Sharuddan da aka gindaya wa matafiya

  • Dole ne gwajin da aka yi wa matafiyan da ke son shiga Najeriya ya kasance ya nuna ba sa dauke da cutar korona
  • Dole ne ya kasance an yi wa matafiyan da ke son shiga Najeriya wannan gwaji kwana hudu, wato awa 72 kafin shiga kasar
  • Ga wasu kasashe, dole ne ya kasance sakamakon gwajin da aka yi wa matafiyan da ke son shiga Najeriya ya kasance ya fito ne daga dakin gwaji da aka amince da shi
  • Dole ne duk wani matafiyi da ke son shiga Najeriya ya kasance ya yi rijista a wannan shafin: https://nitp.ncdc.gov.ng/
  • Dole ne kuma matafiyi ya daura sakamakon gwajin da aka yi masa a shafin da aka rubuta adireshinsa a sama
  • Dole ne matafiya su sake yin wani gwaji a kwana na bakwai bayan isarsu Najeriya, matafiyi na iya zabar inda za a masa gwaji da inda zai karbi sakamakonsa
NCCA

Asalin hoton, NCCA

Bayanan hoto, Duk wanda aka samu da saba ka'idojin da aka gindaya zai fuskanci hukunci

Hukunci

Duk matafiyin da ya shiga Najeriya alhalin sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa yana dauke da cutar korona, ko sakamakon gwajin ya zarce kwana hudu zai fuskanci hukunci, shi ma jirgin da ya dauko shi bai tsira ba.

Idan fasinjan ba dan Najeriya ba ne, za a hana shi shiga sannan a mayar da shi in da ya fito.

Kamfanin jirgin da ya dauko shi ne kuma zai biya kudin mayar da shi gida.

Sannan kamfanin zai biya da tarar Dala 3,500 a kan duk wani fasinja da ya gaza cika ka'idojin da aka lissafa a sama.

Idan kuwa matafiyin dan Najeriya ne za a bashi damar shiga, amma za a tursasa masa killace kai na tsawon mako guda ko makonni biyu, ya danganta.

Sannan shi zai biya kudin killacewa da na gwajin da za a yi masa.

Idan aka gano ba ya dauke da cutar korona bayan mako daya ko biyu da ya yi a killace, za a ba shi damar tafiya gida.

Jiragen da aka amince wa fara yin jigilar fasinja daga Abuja

Ministan jiragen saman Najeriyar ya kuma bayar da sunayen wasu kamfanonin jirgin sama 14 da aka amince wa fara yin jigilar fasinja daga babban birnin kasar Abuja da kuma Legas.

Wasu daga cikinsu sun hada da British Airways da Delta Airlines da Qatar Airways da Ethiopians Airlines da kuma Egypt Air.

Wasu fitattun kamfanonin jirgin sama da ba su samu amincewa ba sun hada da Etihad Airways da Air France.

Karanta cikakken jerin a kasa.

NIGERIA MINISTRY OF AVIATION

Asalin hoton, NIGERIA MINISTRY OF AVIATION

Bayanan hoto, Kamfanonin jirgin sama da za su fara jigilar fasinja zuwa kasashen duniya
NIGERIA MINISTRY OF AVIATION

Asalin hoton, NIGERIA MINISTRY OF AVIATION

Bayanan hoto, Kamfanonin jiragen sama da za su fara jigilar fasinja zuwa kasashen duniya