Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
COVID-19: Sharuɗan da aka gindaya wa ƙasashe 25 kafin barinsu su shiga Saudiyya
Hukumomi a Saudiyya sun fitar da wasu sharuɗa ga ƙasashe 25 wadanda dole sai an cika su kafin ta amince 'yan ƙasashen su shiga cikinta.
Wannan shi ne karon farko da Saudiyya ke fitar da irin wannan sanarwa tun bayan rufe iyakokinta sakamakon bullar cutar korona.
Annobar ta dakatar da kusan komai a kasar ta Saudiyya ciki har da sauya yadda aka yi aikin Hajjin bana.
Mujallar 'Life in Saudi' ta ruwaito cewa cikin sharuɗan da Saudiyyar ta fitar a yanzu akwai bukatar tabbatar da duka fasinjojin da ke cikin jirgin da aka ɗauko daga kasashen ba sa ɗauke da cutar korona.
Sannan dole a ba su takarda ko fom da za su cike domin nuna matsayin koshin lafiyarsu kafin su shiga jirgi da zai kai su Saudiyya.
Kuma wajibi ne duk fasinjoji su mika takardar da suka cike ga sashen da ke sa ido kan lafiya a tashar jirgin da zarar sun isa kasar.
Sharuɗa 5 da aka gindaya wa fasinjojin ƙasashe 25
Dole fasinja ya kasance ba shi da wata alamar matsalar numfashi ko hanta ko wata alama da ke nuna yana dauke ko ya kamu da cutar korona.
Kuma dole duk wani fasinja ya killace kansa na mako guda idan ya shiga Saudiyya.
Kuma wajibi kowanne fasinja ya sauke manhajar Tataman application cikin sa'o'i 8 da ke nuna inda ya sauka, kuma ba zai samu damar barin wannan wuri ba har sai ya cike kwana 7 ne kebe kai, indai ba matsalar lafiya ta taso ba.
A kullum za a buƙaci fasinja ya shiga cikin manhajar Tataman application domin bayar da bayanan yanayin da yake ciki.
Haka zalika, dole kowanne fasinja ya amince da cewa zai biya tarar riyal dubu 500 idan ya karya dokokin da aka saka da kuma zama gidan yari na shekaru biyu.
Ga ƙasashen da aka aike wa waɗannan sharuɗan
- Hadaddiyar Daular Larabawa
- Kuwait
- Oman
- Bahrain
- Egypt
- Lebanon
- Morocco
- Tunisia
- China
- Burtaniya
- Italiya
- Jamus
- Faransa
- Austria
- Turkiyya
- Girka
- Bangladesh
- Philippines
- Malaysia
- Afirka ta Kudu
- Sudan
- Habasha
- Kenya
- Najeriya
- Indonesia