Hotunan Afirka na wannan mako daga ranar 14-20 ga watan Agusta, 2020

An wallafa

Zababbun hotunan Afirka da wasu sassan duniya na wannan mako:

An aerial view taken in Mauritius on August 17, 2020, shows the MV Wakashio bulk carrier, belonging to a Japanese company but Panamanian-flagged, that had run aground and broke into two parts near Blue Bay Marine Park.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Litinin an fitar da hotunan jirgin ruwan nan da ya ci kasa a gabar tekun Mauritius inda ya dare biyu...
Workers collect leaked oil at the beach in Riviere des Creoles on August 15, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ... ranar Asabar ta makon jiya ma'aikata suka fitar da man fetur da ya zube daga jirgin ruwan...
A picture taken on August 15, 2020 shows iridescence on the water at the beach in Petit Bel Air.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, .... Man fetur daga cikin jirgin ruwan mai suna MV Wakashio ya haddasa lalacewar muhalli.
A man watches local TV coverage of resignation of Malian President Ibrahim Boubacar Keita at a printing shop near the Independence Monument in Bamako, Mali.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Talata 'yan kasar Mali sun kalli talbijin inda suka ga jawabin shugabansu na sauka daga mulki...
Armed members of the FAMA (Malian Armed Forces) are celebrated by the population as they parade at Independence Square in Bamako on August 18, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ... Sojojin Mali da suka yi bore sun kama Shugaba Ibrahim Boubacar Keitakuma sun yi ta zirga-zirga kan titunan babban birnin kasar Bamako.
A farmer rides on his horse during a protest against farm attacks in Mookgophong on August 18, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Talata manoman Afirka ta Kudu sun yi zanga-zanga kan hare-haren da ake kai wa gonakinsu. A watan Maris aka kai wa mutum biyu da ke cikin hoton nan, Alwyn van Zyl, da mai dakinsa Pauline. Matar ta tsira amma mijin ya mutu.
Morocco's Soufiane EL Bakkali (C) competes in the men's 3000metre steeplechase event during the Diamond League Athletics Meeting at The Louis II Stadium in Monaco on August 14, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Juma'a dan kasar Morocco Soufiane EL Bakkali ya fafata a tseren tsallake shamaki da aka yi a birnin Monaco.
A priest administers the Holy Communion during the service at the Notre Dame du Congo cathedral in Kinshasa on August 16, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Lahadi a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, mabiya darikar Katolika sun yi adduo'i karon farko a coci tun bayan da aka kakaba dokar kulle a watan Maris.
Algerian volunteers desinfect the prayer hall ahead of the noon prayer at the El Fateh mosque in the El Afia de Kouba neighbourhood of the capital Algiers, on August 15, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Asabar, masu aikin sa kai sun tsaface masallacin El Fateh da ke Algiers , babban birnin Algeria, domin rage yaduwar cutar korona.
A policeman, mask-clad due to COVID-19 coronavirus pandemic, watches as people cool off in the water at el-Kettani beach in the Bab el-Oued suburb of Algeria's capital Algiers on August 15, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wani bangare na birnin, mutane da dama sun yi wa bakin teku tsinke domin shakatawa.
A Senegalese man cleans himself along the coastline in Bargny on August 15, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ... A ranar, a wani bakin tekun. Wannan karon a kauyen Bargny da ke kasar Senegal.
People bathe in the Mediterranean sea water off a beach in Libya's capital Tripoli near sunset on August 18, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Talata mutane sun shakata a bakin teku da ke Tripoli, babban birnin Libya, a yayin da ake fama da yawan daukewar wutar lantarki.

Pictures from AFP, Getty Images, EPA and Reuters.