Death Valley: Yadda aka yi rana mafi zafi a tarihin duniya a wannan yankin na Amurka

A woman drinks water from a plastic bottle on June 20, 2017 in Quimper, western France

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsananin zafi na hana jikin dan Adam samar da daidaito a bangaren zafi
An wallafa

Kun taba tunanin yadda rayuwa take kasancewa a wurin da zafinsa ya kai 54.4 a ma'aunin celsius?

Lallai ba sai an yi tunanin yanayin ba domin ya riga ya faru.

Wannan ne matsanancin zafi mafi yawa da aka taba aunawa a doron duniyarmu.

An kuma sami haka ne a wani kebabben wurin shakatawa da ke cikin wani kwari mai suna Death Valley (wato Kwarin Mutuwa) da ke jihar California a Amurka da misalin karfe 3:41 na ranar Asabar 16 ga watan Agustar 2020.

To yaya zafin ya kasance? Barndi Stewart ma'aikaciya ce a gandun dajin mai suna Death Valley National Park, kuma ta bayyana zafin tamkar a tattara na'urorin busar da suma irin wadda mata kan yi amfani da su a wurin gyaran gashi, kuma a kunna su gaba dayansu a lokaci guda.

"Na tabbatar muku cewa dukkanmu mun kosa zafin ya wuce," in ji ta.

Me ya sa tsananin zafi ke iya mana lahani?

A man fills plastic containers with water on a cart drawn by a donkey

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani bincike ya ce yankunan Indiya da kudu maso gabashin Asiya na cikin waɗanda tsananin zafi zai yi mummunan tasiri ga lafiyar mazauna yankunan

Tsananin zafi na iya yin tasirin kan kowa, amma rashin ruwa a jiki da kasalar da zafi kan haifar da bugun zafin na iya saka dan Adam cikin hatsari, musamman masu ciwon zuciya da na ƙoda da waɗanda suka shafi numfashi. Yana kuma shafar kananan yara da manyan mutane.

Irin wannan tsananin zafi yana aukuwa ne a lokaci zuwa lokaci kuma zuwa yake kamar bugun tsananin zafi ya kuma wuce.

A wannan karon ya shafi yankin gaɓar teku da ke yammacin Amurka ne.

Masu rauni kan iya shiga wani mawuyacin hali domin zafin kan rage damar da jikin dan Adam ke da ita ta daidaita yawan zafi ko sanyin jikinsa ta yadda zai zauna lafiya kamar yadda aka tsara," in ji Timothy Hewson, wanda ke jagorantar wata cibiyar nahiyar Turai mai bincike kan tasirin matsakaicin yanayin duniya.

Me ya sa tsananin zafi ke da hatsari?

Death Valley landscape

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yankin Death Valley makekiyar hamada ce mai ramuka da tsibin yashi mai tarin yawa

Kwarin Death Valley ya fuskanci wani yanayin da aka fi sani da busasshen zafi.

Kusan iskar da ta rika busawa a yankin ba ta da ruwan da ya wuce kashi 7 cikin 100.

Akwai kuma wasu abubuwa kamar rashin kadawar iska mai karfi da ka iya kara yawan zafi.

Yaya ake auna sanyi ko zafi?

The Sun sets on a beach as two people sit by a lookout tower

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsananin zafi yafi kashe Amurkawa fiye da guguwa ko ambaliyar ruwa

Yawancin cibiyoyin da ke auna yanayi a fadin duniya na amfani da na'urar thermometer biyu.

Ta farko tana auna zafin iska ne, inda ta biyu kuwa tana auna yawan ruwan da ke cikin iskar da ke kadawa ne.

Hatsarin zafi da rashin ruwa

A man drinks water from a bottle in front of a hot Sun

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani sabon bincike ya nuna hatsarin tsananin zafi ta rashin ruwa a cikin iskar da ke kadawa a fadin duniya

Ga dan Adam, tsananin zafi da rashin isasshen ruwa a cikin iska na iya yi musu lahani matuka a wannan lokacin da duniya ke dumama.

Ga yadda al'amarin yake a zahiri: Jikinmu na bukatar sanyi ko zafikar ya zarce ko ya kasa maki 37.5 na ma'aunin celsius, ko da kuwa ana tsananin zafi ko sanyi ne.

Idan zafi ya karu, tilas jiki ya fara rage yawan ruwan da ke cikinsa ta hanyar yin zufa.

Amma idan akwai ruwa mai yawa a cikin iska, jikin dan Adam na kasa fitar da ruwan ta hanyar zufa - wanda ka iya halaka mutum cikin sa'a shida idan ba a sami yanayi mai daidaita zafin jikin ba.

A waɗanne yankuna aka fi samun tsananin zafi?

A man and two children in traditional dress stare across water at a city in the Gulf

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An fi samun tsananin zafi a yankin tekun Gulf da ƙasashen da ke kusa da shi

A ƴan shekarun nan bincike ya nuna cewa akwai wuraren da tsananin zafi ya fi aukuwa.

An taba auna tsananin zafi har sau 14 a biranen Dhahran da Dammam na Saudiyya da Doha na Qatar da Ras al Khaimah na Hadaddiyar Daular Larabawa.

An kuma sami irin wannan zafin a wasu yankuna na kudu masu gabashin Asiya da kudancin China da nahiyar Afirka da yankin Caribbean.

Yankin kudu maso gabashin Amurka ma ya sha samun irin wannan matsanancin zafin kamar gabashin Texas da Louisiana da Mississippi da Alabama da kuma yankin Panhandle na Florida. Biranen New Orleans da Biloxi ma ba a bar su a baya ba.

Tsananin yanayi mai ban tsoro

Firenado in Lassen County on 15 August

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yayin da zafi ke karuwa a California, an hango wata guguwar wuta a karamar hukumar Lessen ta jihar

Mutanen garin Furnace Creek da ke tsakiyar kwarin Death Valley mafi zafi a duniya ba su da zabi. Ya zama musu dole su yi hakuri da matsanancin zafin da ke karuwa a yankin nasu.

Garin na tsakiyar wani kwari ne da ke da zurfin kafa 280 a karkashin ma'aunin ruwan teku - wanda wasu manyan tsaunuka suka kere shi ta kowane bangare.

Shi ya sa mutanen garin su 570 suka fi son zama cikin gidaje da wuraren aikinsu, kuma dukkansu na amfani da na'urar sanyaya daki ne idan ba a dauke hasken lantarki ba.

Amma yawancin mutanen garin sun ce sai sun hau bisa tsaunukan da ke zagaye da garin nasu ne suke samun sauki daga tsananin zafin da ya lullube yankin.