Ga yadda matsalar tattalin arzikin da Birtaniya ta shiga zai shafi ƴan Afrika

Black UK students

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A karon farko cikin shekaru 11 Birtaniya ta shiga matsalar tattalin arziki, kuma ana ganin wannan wani babban al'amari ne da zai shafi mutane da dama gida da waje.

Tattalin arzikin ya ragu da kusan kashi 20.4 idan aka kwatanta da watanni uku na farkon shekara.

Mutane da dama na rububin sayen kayayyaki yayin da kantina ke rufewa, sannan kuma masana'antu da kamfanoni ke rage yawan kayayyakin da suke samarwa.

Hukumar ƙididdiga ta ce rufe shaguna da otel-otel da wuraren cin abinci da makarantu da kuma wurin gyaran motoci ya shafe su.

Wannan ne ya haifar da taɓarbarewar tattalin arzikin Birtaniya - wanda tattalin arzikin bai taɓu ba tun shekarar 2009.

Ko ya tasirin taɓarbarewar tattalin arzikin Birtaniya?

Ayyuka/Kuɗaɗe

Mutane da dama za su iya rasa ayyukan yi, wasu kuma da dama yana da wahala su ƙara masu muƙami ko kuma ba ƙarin albashi. Ga ƴan Afirka da suke da ɗan uwa a ƙasashen waje, wannan zai iya shafarsu inda yawancin ƙasashe sun fi ba ƴan kasarsu muhimmanci kafin ƴan wata ƙasa.

Idan har ƴan Afirka a Birtaniya suka kasance ba kasuwanci, ko kuma suka rasa ayyukansu, akwai yiyuwar za su dakatar da kuɗaɗen da suke "aikowa gida."

Za a kai lokacin da ma za su fara neman taimako daga gida.

Ilimi/Ɗalibai

Ɗalibai ƴan Afirka da suke son zuwa karatu a Birtaniya za su ga sauyi ta ɓangaren katsewar taimako da suke samu. Lokacin da aka shiga matsalar tattalin arziki a 2009, makarantun Birtaniya sun datse yawan kuɗaɗen da suke taimaka wa dalibai.

Akwai yiyuwar ƙara kuɗaɗen makaranta.

Ga ɗaliban Birtaniya za su iya shiga garari na rashin samun aikin yi. Ga waɗanda ke son shiga makaranta, matsalar tattalin arzikin zai iya sa ɗage har zuwa wani lokaci saboda babu tabbacin samun kuɗade na tafiyar da makarantun.

Biza

Babu tabbas ko za a iya ƙara kudaden bizar Birtaniya ko kuma ya ragu. Ko kuma bizar za ta yi wa ƴan ƙasashen waje wahalar samu da ke son shiga Birtaniya.

Passport

Asalin hoton, Nigeria Immigration Service

Ƙaruwar talauci

Wasu za su iya cewa talacin da taɓarɓarewar tattalin arzikin za ta haifa za ta kuma ƙara yaɗuwa tsakanin mutane da waɗanda ke ƙarkashinsu. Wannan saboda wani lokaci yana da wahala cikin lokaci a farfaɗo.

Gidaje

Farashin gidaje a Birtaniya zai iya raguwa, yayin da mutane da dama suke buƙatar kuɗi inda wannan masu zuba jari daga waje ne za su fi morewa - ko da kuwa daga Afirka ne.

Amma masana na ganin masu gidaje za su iya ƙin sayar da ƙadarorinsu. Don haka ba tabbas.

Khafi Kareem

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Khafi Kareem da ta yi fice a Big Brother Naija ta yanke shawarar yin zamanta a Ingila

Me ya faru a taɓarɓarewar tattalin arziki a 2009?

Raɗadin tattalin arzikin bai yi wa kowa daɗi ba. Wato kowa ya ji a jikinsa kuma jin jikin ba zai kasance kamar kowa ba domin wasu ba su sha wahala ba.

Misali a 2009, yawancin ƴan Birtaniya masu gidaje da suka yi haƙuri sun ci riba lokacin da aka farfado daga matsalar tattalin arzikin.

Haka kuma, kuɗaden ruwa na gidaje sun ragu, wannan kuma ya sa mutane suna kashe kudi sosai.

Wannan waɗanda suka suke dogaro da gwamnati ko kuma ma'aikata, matsalar ta fi shafarsu sosai.

Grey line wey dey