Hotuna: Yadda tsananin zafi ya addabi mutanen Iraƙi

An wallafa

'Yan ƙasar Iraƙi na ta ƙoƙarin sararawa ta hanyar samun abu mai sanyi sakamakon irin zafin da ake tafkawa a Gabas Ta Tsakiya.

Yanayin zafi a Bagadaza babban birnin ƙasar ya kusan kai matakin digiri 52 a ma'aunin Celcius a ranar Talata, wanda wannan shi ne yanayi mafi zafi da birnin ya taɓa fuskanta.

An ce zafin ya wuce matakin digiri 51 a ma'aunin Celcius a ranar Laraba.

Jama'a da dama sun yi zaman su cikin gida, wasu kuma a tsakiyar birnin Bagadaza suka nemi mafaka ƙarƙashin wani famfo mai feso ruwa da aka tanada.

Sai dai zafin ya ƙara matsin lamba ga baitul malin ƙasar wanda tun dama yana cikin matsi.

Yankewar wutar lantarki a Bagadaza ya ja mutane da dama suna amfani da janareto domin samun wutar da za su kunna fankoki da kuma na'urar sanyaya ɗaki.

Wannan lamarin ya jawo ran mutane da dama ya ɓaci wanda hakan ya jawo zanga-zanga a farkon makon nan.

Akalla masu zanga-zanga biyu ne suka mutu a ranar Litinin, hukumar kare haƙƙin bil adama ta Iraƙi ta bayyana cewa sama da mutum 20 jami'an tsaro suka kashe yayin zanga-zanga.

Ƙasar ta yi fama da raguwar farashin man fetur tun bayan ɓullar annobar korona.

Sama da mutum 118,000 suka kamu da cutar a Iraƙi inda kuma mutum 4,606 suka mutu a ƙasar, kamar yadda ƙididdiga daga jami'ar Johns Hopkins ta nuna.

Duka hotunan na da haƙƙin mallaka.