Coronavirus a Tanzania: 'Cutar ta raba kawunan iyalaina'

An wallafa

Wakilin BBC a ƙasar Tanzania, Sammy Awami ya wallafa cewa matakan da Shugaban Tanzania, John Magufuli ke ɗauka domin yaƙi da cutar korona waɗanda suka fi alaƙa da addini sun raba kan mutanen gidansu.

Tun bayan da aka samu mutum na farko da ya kamu da cutar korona a Tanzania a watan Maris, 'yan uwa da abokan aikina da ke zaune a ƙasashen waje suka riƙa damu na da kiraye-kiraye.

Suna ta mamaki: ta yaya ƙasar da ba ta saka dokoki masu tsauri ba amma ta tsira daga annobar da ta karaɗe kowane lungu da saƙo na duniya.

Hatta mu da muke zaune a ƙasar abin na ba mu mamaki.

Shugaba Magufuli na cikin 'yan ƙalilan ɗin shugabannin da suka ƙi saka wasu dokokin kulle sannan ya ce sauran ƙasashe ma sun firgita ne kawai.

Duk da sukar da ake yi wa shugaban game da halin ko-in-kula da yake nunawa wurin yaƙi da cutar, ƙasar ta tsallake ɗaruruwan mace-mace da ake gani a wasu ƙasashe.

Babban abin da ya fi ɗaure wa al'umma kai shi ne, babu wanda ya san yadda aka yi hakan ta faru.

'Addu'a ce babban magani'

Ɗaya daga cikin irin waɗannan maganganu ita ce babu alƙaluman da za mu kalla don yin lissafi.

Shugaba Magufuli ya zaɓi ya saka dokar kulle kan alƙaluman ba kan mutane ba.

A cewar Aidan Eyakuze, wani mai sharhi: "Da gangan ya mayar da ƙasar aiki cikin duhu game da alƙaluma."

Wasu likitoci uku da na yi magana da su amma ba su bari naɗi muryarsu ba, sun faɗa mani cewa ba a cika asibitoci ba.

Wasu na tsoron su faɗi abin da ya ci karo da abin da gwamnati ke faɗa saboda kada a hukunta su.

Shugaban ƙungiyar likitocin Tanzania, Dr Elisha Osati ya ce babu wata rufa-rufa, amma yanzu yana so ya tsaya takarar ɗan majalisa ƙarƙashin jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi.

Yayin da likitoci ke shawartar mutane su ɗauki matakan kariya saboda haɗarin da cutar yi a rayuwarsu, shugaban ƙasar ya ce jama'a su yi addu'a su ci gaba da harkokinsu kawai.

A matsayinsa na mabiyin Ɗarikar Katolika, Magufuli ya faɗa wa wani taron coci cewa "addu'a ce babban magani" sannan kuma "an kawo ƙarshen cutar cikin ikon Allah".

Mafi yawan 'yan uwana magoya bayan Magufuli ne kuma da yawansu cikakkun Kiristoci ne.

'Dandalin WhatsApp ya zama filin yaƙi'

Yadda aka riƙa siyasantar da batun korona a ƙasar ya sa abu ne mai wuyar gaske na iya shawo kan 'yan uwana su ɗauki matakan kariya.

Zauren WhatsApp na iyalin gidanmu ya zama wani filin yaƙi.

An riƙa yaɗa wasu rahotanni da ke goyon bayan shugaban da kuma shawarwarin da mutane ke cewa a ci gaba da harkoki kuma a yi wa ƙasar zaton alkairi.

Sannan suna jin tsoron abin da za su rasa idan aka rufe kasuwanni da harkoki.

Mu ɗauki 'yan uwana guda uku misali, dukkaninsu fasto-fasto ne.

Su a wurinsu coci ba wai wuri ne na neman taimakon Allah ba kawai, ita ce babbar hanyar samun kuɗinsu.

'Na yi ƙoƙarin wayar da kan yayyena'

Na ƙirƙiri zaure a WhatsApp, inda na saka manyan yayyena a ciki domin wayar musu da kai game da annobar tare da roƙonsu da zauna a gida.

Sun ma saurare ni ne, su zauna a gida su rasa abin da za su ci? Ko kuma su bi shawarar shugaban ƙasa ta yin addu'a da ci gaba da harkoki?

'Ƙirƙirar sabon abokin gaba'

Tabbas sun yarda cewa cutar tana da haɗari. Sai dai kuma sun yarda da addu'a - musamman ma idan ta haɗo da hanyar cin abincinsu.

A irin wannan ƙasa da kowa yake hannu baka hannu ƙwarya kuma kowa yake da addini, shugaban ƙasar ya yi amfani da addini don yaɗa manufofinsa.

Kazalika shugaban ya tabbatar da cewa ya samo wani sabon abokin gaba a lokacin yaƙi da cutar - Turawan Yamma.

Ya sha kiran Turawan da suna "mabeberu" wato "bunsuru".

An ƙirƙiro sunan ne tun lokacin gwagwarmayar neman 'yancin kai. Sunan ya shahara tsakanin manyan mutane kamar iyayena.

Mista Magufuli ya yi imanin cewa "mabeberu" da 'yan korarsu na amfani da annoabar korona domin hana ƙasar cimma muradunta na tattalin arziki.

A ɗaya daga cikin maganganunsa da ya yi, ya nuna cewa Turawan Yamma ka iya saka cutar a cikin kayan da ake shigowa da su cikin ƙasar domin shafa wa Tanzaniyawa.

Ya riƙa tuna wa mutane zamanin cutar ƙyanda da kuma farkon ɓarkewar cutar HIV/Aids, yana mai tuna musu yadda iyaye suka riƙa hana 'ya'yansu ziyartar maƙota saboda kada su kamu da cutukan.

Abin da mutane ke nunawa a yanzu shi ne: "Idan mutane ba faɗuwa suke yi ba a titi, to a ci gaba da harkoki kawai."

Abu ne mai haɗari amma mutane a nan suna ƙoƙarin karɓarsa sannan su yi fatan gwamnati gaskiya take faɗa musu.