Dr Stella Emmanuel: Abin da ya sa Facebook ya cire bidiyon likitar Afirka da ta yaɗa maganin hydroxychloroquine

Dr Stella Immanuel

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto, Dr Stella Emmanuel ta ce mutum fiye da 350 ne suka yi amfani da hydroxychloroquine
An wallafa

Facebook, Twitter, Periscope da wasu shafukan sada zumunta sun cire wani bidiyo da ya yadu sosai a shafukan zumunta wanda ya nuna wata liita 'yar Afirka da ta yi ikirarin cewa ta yi amfani da maganin hydroxychloroquine, zinc, da kuma maganin da ke kashe bakteriya Zithromax wajen maganin Covid-19 a masu fama da cutar a Amurka.

An cire bidiyon ne bayan kusan mutum miliyan 14 sun kalle shi kuma Shugaba Donald Trump ya sake yada bidiyon da aka wallafa a Periscope.

Dr Stella Emmanuel, wacce ma'aikaciyar lafiya ce a matakin farko a birnin Houston, ta shaida wa manema labarai cewa ta yi amfani da maganin wajne yi wa mutum sama da 350 maganin cutar korona

A cewar Dr Immanuel, wasu daga cikin mutanen da ta bai wa maganin tsoffi ne, wasu kuma suna da cutar hawan jini da tarin asthma.

"Na bai wa [masu fama da cutar] hydroxychloroquine, na ba su zinc, na kuma ba su Zithromax kuma dukkansu sun warke, " a cewar Dr Stella.

Cutar korona na ci gaba da yaduwa sosai a duiya, inda yanzu haka mutum fiye da miliyan 16 a kasashe 188 suka kamu da ita. Mutum kusan 650,000 ne suka mutu sanadin cutar.

Me ya sa Facebook ya cire bidiyon?

Daraktan sadarwa na Facebook Andy Stone ya wallafa sakon Twitter cewa: "Mun cire bidiyon ne saboda ana yada labaran karya kan maganin cutar korona a cikinsa."

Me Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce a kan hydroxychloroquine?

Anti-malarial drugs

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An samar da maganin ne da farko don cutar maleriya

Ranar 4 ga watan Yuli Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar cewa ta tsayar da gwada magunguna hydroxychloroquine da lopinavir/ritonavir.

Ta dakatar da shi ne saboda gwajin da ta yi a kansa ya nuna cewa ba ya warkar da Covid-19.

Binciken Hukumar ya nuna cewa hydroxychloroquine da lopinavir/ritonavir ba sa hana masu dauke da Covid-19 mutuwa idan aka kwatanta da sauran magungunan da ake ba su.

Wace ce Stella Immanuel?

Dr Stella Immanuel masaniya ce ta lafiya a matakin farko a birnin Houston na jihar Texas. Tana aiki a cibiyar kiwon lafiya ta Houston.

A cewarta, ta halarci makarantar horas da ma'aikatan lafiya ta Yammacin Afirka da ke Najeriya, ko da yake ba ta fadi takamaimai sunan makarantar ba.