Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: 'Rayuwa a Ghana ta fi ta Turai da Amurka daɗi'
A cikin jerin wasikun da marubuta ke aiko wa BBC daga Afirka, wata minista a Ghana, Elizabeth Ohene ta yi rubutu kan yadda 'yan Ghana suka daina rububin zama a kasashen waje saboda cutar korona.
Fiye da shekara 20 da suka shude mun ci gaba da yin haka, ba wai don ba mu da yadda za mu yi ba ne, saboda ya zame mana halayya ne.
Yanzu masu matsakaitan hali na kokarin ganin sun tura matansu zuwa kasashen waje kamar Amurka domin su haihu, sannan wasu kan yi bara ko sata duk don su tura 'ya'yansu karatu a Amurka ko Birtaniya, kuma su kan basu shawarar cewa su ci gaba da zama idan sun kammala karatu.
Babu jumillar adadin yawan 'yan kasar Ghanan da ke zaune a kasashen duniya, ballantana a san ma me suke yi a can.
Ko shakka babu wasu daga cikinsu na yin abin da ya dace wanda har kasar ma kan yi alfahari da su.
To amma kuma akwai 'yan kasar Ghanan da ke zaune a wasu kasashen tare da sanin cewa an sanya musu idanu, kuma suna kokarin cika sharudan da ya kamata su cika don zama a wata kasa.
A kodayaushe suna rayuwa ne a cikin shirin ko-ta-kwana, amma kuma mun san suna can.
Ta hanyar ayyukan da suke yi a can, su kan aiko da kudi domin taimakawa iyayensu.
Abin kunya ne a ce kana da dan uwa a kasar waje a ce ba zai iya cika burin 'yan uwansa ba musamman wajen gudanar da kayataccen bikin jana'iza.
Ga wadanda suka samu cikakkiyar takardar shaidar zama ko izinin shiga wata kasa wato visa, kan tsara zuwa gida hutu kamar su zo su yi bikin Kirsimeti a gida.
Idan suka zo ganin gida, sai su rika yin abubuwa kamar bushasha da kudi - kamar ba wadanda suka sha wuya kafin su samu kudin ba - ba za ka taba jin sun ce ai suna shan wuya a can ba.
Suna yin hakan ne don jan hankalin sauran matasa a kan rayuwar Turai.
Ana nan, katsam sai ga cutar korona, wannan ya sa an rufe wuraren da matasan ke zuwa domin yawon bude ido a kasashen Turai.
Wannan ya sa sai 'yan Ghanan da ke kasashen Turai suka ji ba sa sha'awar zama a can, wannan ta sa aka fara dawowa gida.
Ko da suka dawo gida Ghana, sai suka ga kasarsu da ma wuraren shakatawar da ke a kasar sun fi zama abin sha'awa.
Yayin da cutar korona ke ci gaba da yaduwa, tunanin 'yan kasar Ghana da ke kasashen waje na cewa sun fi kowa sa'a sai ya fara canzawa.
Ba wai don cewa wasunsu na mutuwa a wasu kasashen saboda cutar korona ba, saboda damuwar da suke da ita na son dawowa gida.
Idan dai har za mu gano cewa mutane da dama a manyan biranen Ghana na shan wuya wajen samun abin da zasu ci a lokacin kullen korona, to zamu iya gano cewa ya yanayin 'yan Ghanan ya ke a kasashen waje?
Masu gidajen hayar da suka ba wa irin 'yan kasar Ghanan da ke kasashen waje haya, a yanzu suna son mutanen su kasnace suna da cikakkiyar shaidar shiga cikin kasa wato visa.
Yayin da aka rufe wuraren kasuwanci a kusan ko ina saboda cutar korona, yawancin 'yan kasar Ghana a kasashen waje sun gano cewa shayi madara ne.
Muna nazari a kan yadda ake wulakanta tare da fallasa mutanenmu.
Yanzu an gano cewa, yawancin matan da ke zuwa kasashen waje su yi aiki kamar na reno a Lebanon da sauran kasashen Larabawa na fuskantar abin da wani dan kasar Ghana ba zai dauka ba.
Bullar annobar korona ta sa mun sauya tunaninmu, yanzu mutane na son komawa gida amma kuma an rufe iyakoki.
'Yan Ghanan da ke zaune a gida na ganin cewa daga kasashen waje aka kawo musu cutar, ma'ana matafiya da suka dawo daga kasashen waje su ne ke kawota.
A yanzu akwai jiragen da ke kwaso mutane daga wata kasa su mayar da su kasarsu, amma kuma farashin ya yi tsada.
Zaman kasashen waje a yanzu dai kamar ya zama ba shi da dadi.