Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda al'ummar Legas ke fama da rufe Gadar Third Mainland
Masu ababn hawa a jihar Legas sun fara ji a jikinsu saboda rufe Gadar Third Mainland da aka yi tun daga daren Juma'ar da ta gabata.
Yawanci masu shiga motocin haya sun yi korafin cewa an kara musu kudin mota, ga kuma cunkoson ababen hawa inda manyan motoci duk sun cike hanyar, wasu ma sun tsaya a yadda suke don kafin a samu a wuce abin da wuya.
Ma'aikatar kula da ayyuka da gidaje ta kasa ce ta sanar da cewa za a fara gyaran gadar ta Third Mainland, wadda ita ce ta biyu a girma a Afrika, kuma za a shafe watanni shida ana wannan aiki.
Wakilin sashen BBC Pidgin da ya zaga gadar a safiyar Litinin ya ce, akwai ababen hawa a gadar da ke wucewa amma kuma babu cunkoso saboda mutane sun sauya hanyar da suke bi wadda suke ganin za su fi samun saukin wucewa.
A yanzu haka, an bude hanyar da ta tashi daga Mainland zuwa Island ta kan hanyar Mainland domin mutane su rinka wucewa.
Yaya mutane za su yi da wannan mataki na rufe gadar?
Daniel, lauya ne ya kuma shaida wa shashen BBC Pidgin cewa, ya bar gidansa kusan karfe 5:30 na safe, tafiyar da zai yi ba ta fi ta minti 15 ba, amma sai da ya kai har karfe bakwai na safe yana hanya.
Ya ce, samun wajen ajiye mota ma mutum ya taka babu, saboda manyan motoci sun tare hanya, bai kai inda zai je ba sai karfe tara na safe.
Game da wata hanya da gwamnatin Legas ta ce mutane za su iya bi, Barista Daniel ya ce hanyar ta yi kusa da ruwa don haka akwai hadari bin ta saboda a yanzu lokaci ne na damuna komai na iya faruwa.
Wani mutum mai suna Andrew, ya ce hanyar ta cunkushe musamman yadda aka samu cunkoson manyan motocin da ke zuwa Apapa.
Wata mata da ta hau motar haya ta shaida wa BBC cewa, cunkoson ababen hawa ya yi yawa, ta bar gida tun misalin karfe shida na safe, ta tarar an kara kudin mota sosai.
Ga hanyoyin da aka bayar da zabi da mutane za su rinka bi a farkon watanni ukun da za a fara gyaran gadar.
Ga wadanda za su taho daga Lekki da Ikoyi da Obalende da kuma Legas Island, gwamnatin tarayya ta shawarce su da su rinka bi ta Gadar Carter su shiga Iddo sai Oyingbo sai Ebute Metta sannan daga nan sai su nemi hanyar inda za su je.
Amma an shawarce su cewa ka da su bi ta Clinic Way ta cikin Adekunle saboda an kulle ta wuraren.
Wadanda suka taho kuma daga Victoria Island da Bonny Camp, an shawarce su su bi ta Gadar Independence zuwa Onikan sai su bi ta gadar Obalende su shiga Oyingbo zuwa Ebute Metta.