Afrika Ta Kudu: An kama fursunoni 68 da suka tsere daga gidan yari

Jami'an tsaro sun kama duka 'yan fursunan da suka tsere daga gidan yari a Afrika Ta Kudu a ranar Juma'a.
An dai yabi gandirebobin gidan yarin sakamakon shafe kusan kwanaki biyu suna bin sawun 'yan fursunan da suka tsere.
Rikicin da ya sa suka tsere ya faru ne bayan fursunonin sun sha ƙarfin gandirebobin da ke gidan yari na Malmesbury yayin wani atisaye.
Hakan ya sa fursunonin suka rufe gandirebobin cikin ɗaki kafin suka saki 'yan uwansu da ke tsare sa'annan suka haura ta katanga kuma suka gudu, in ji hukumomi.
Rahotannin da aka bayar a baya dai sun ce fursunonin sun tsere ne yayin da ake kan hanyar kai su wurin shari'a.
Hukumar gyara ɗabi'u ta Afrika Ta Kudu a baya dai ta ce fursunoni 68 ne suka tsere, sai dai daga baya ma'aikatar shari'a ta ƙasar ta bayyana cewa jumullar mutum 68 ne suka gudu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Ya lamarin ya faru?
A ranar da abin ya faru, gandirebobi 20 ne kacal ke aiki a ranar inda suke kula da fursunoni 451, kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga hukumar gyara ɗabi'u ta ƙasar a ranar Juma'a.
"Fursunonin sun sha ƙarfin gandirebobin, suka ƙwace mukullan, sa'annan suka rufe jami'an uku cikin fursuna, sa'annan suka buɗe sauran ɗakunan kafin suka haura ta katanga." in ji hukumar.
Gandirebobi tara sun "ɗan ji rauni da kuma gurjewa" yayin lamarin.
Tuni dai ministan shari'a na ƙasar Ronald Lamola ya gode wa jama'ar yankin da lamarin ya faru domin irin bayanan da suka ba su har hakan ya kai aka kama fursunonin.
Kafar yaɗa labarai ta News24 ta ruwaito shi inda yake cewa za a hukunta duk waɗanda suka tsere.













