Coronavirus a Amurka: Trump ya ce cutar za ta 'ci gaba da yaɗuwa'

An wallafa

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa cutar korona "za ta ta'azzara kafin a samu sauƙi" a ƙasar, a yayin da ya dawo da taron da yake gudanarwa kan cutar.

Mista Trump ya kuma buƙaci dukkan Amurkawa su riƙa sanya takunkumi, yana mai cewa "zai zama kariya" kuma sanya shi tamkar nuna "kishin ƙasa ne".

Shugaba Trump, wanda ba ya sanye da takunkumi a lokacin jawabin, a baya ya yi watsi da batun sanya takunkumin yana mai cewa yin hakan rashin tsafta ne.

Rahotanni sun ce masu ba shi shawara ne suka matsa masa ya ɗauki matakin sakamakon ci gaba da yaɗuwar cutar a dukkan faɗin Amurka.

Trump ya daina gudanar da taron kowacce rana kan cutar korona ne bayan a watan Afrilu shugaban na Amurka ya ce sinadarin da ake wanki da shi yana iya maganin cutar idan aka yi wa masu cutar allurarsa.

A cikin jawabinsa a karon farko bayan ya dakatar da yin taron a Fadar White House kan annobar ta korona, Shugaba Trump ya yi gargadi ga Amurkawa inda ya bukaci matasa su kaurace wa shiga taron jama'a.

Ya ce za a ɗauki lokaci kafin a rabu da cutar gaba daya.

Mista Trump ya riƙe takunkumi a hannunsa inda ya shaida wa manema labarai cewa zai saka tare da kuma yin kira ga Amurka su dinga sakawa idan har ba za su iya bayar da tazara tsakaninsu ba.

Cutar korona dai na ci gaba da yaɗuwa a Amurka inda a kullum ake bayar da rahoton dubban mutane da suka kamu da cutar wadda kawo yanzu ta kashe mutum 140,000 a ƙasar.

Mista Trump - fiye da sau ɗaya ya ce cutar korona 'yar kasar "China ce".

Shugaban kasar yana fuskantar babban kalubale daga ɗan takarar jam'iyyar Democrat, Joe Biden a yunƙurin da yake yi na sake lashe zaɓen Amurka da za a yi a watan Nuwamba, a cewar ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a.

Mista Biden ya zargi Mista Trump ranar Talata da gazawa a yunƙurin shawo kan cutar ta korona.

Ƴan adawa kamar shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi sun ce yadda Trump ya dawo yana saka takunmmu a yanzu har da kuma yin kira a dinga sakawa yanzu ya tabbatar da kurakuransa kan yadda ya kamata ya yaƙi cutar.