Dubban masu zanga-zanga a Israi'la sun bukaci fira minista Netanyahu ya sauka

An wallafa

Dubban 'yan Israi'la sun gudanar da zanga-zanga a Tel Aviv, don nuna adawa da abin da suka kira kangin tattalin arziki da salon gwamnati na yaki da annobar korona ya tsunduma al'umma ciki.

Matasa da dama sun cika maƙil a dandalin taro na Robin Square sanye da takunkumai, sai dai ba tare da bayar da tazara ba.

A birnin Kudus kuwa daruruwan mutane sun taru a kofar gidan Fira minista Benjamin Netanyahu, suna kiran ya sauka daga kan kujerarsa.

'Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi, domin tarwatsa dubunnan masu zanga-zangar, abin da ya rikide ya koma tashin hankali.

Masu zanga-zangar na kuma nuna damuwa kan yadda diyyar da gwamnati ke bayarwa ba ta isa gare su a kan lokaci.

Kananan 'yan kasuwa da ma'aikata masu zaman kansu da fitattun taurari ne suka shirya zanga-zangar, da ta samu tabarrakin jama'ar gari.

Mutane da dama a kasar sun tagayyara, kuma suna nuna takaici a kan yadda dokokin da aka kafa na yaki da cutar ta korona a kasar ke ci gaba da janyo musu wahala.

Yayin da ma'aikatan gwamnati ke samun tallafi, su kuwa ma'aikata masu zaman kansu cewa suke har yanzu ba a cika musu alkawarin basu tallafin da aka musu ba.

Ranar Jumma'ar da ta gabata dai Frai ministan kasar Benyamin Netanyahu ya gana da 'yan gwagwarmaya domin tattauna matsalolinsu.

Ya shaida musu cewa gwamnatinsa, za ta ci gaba da kokarin biyan bukatun Jama'a, da suka hadar da biyansu alkawuran da aka musu na jin kai.

Tun a tsakiyar watan Maris ne hukumomi a Israila suka kakaba dokar kulle, domin yaki da annobar korona.

Tun daga wancan lokaci zuwa yanzu, alkalumma sun nuna cewa an samu karuwar rashin aiki a kasar da kaso 21.