Kanye West ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban Amurka na 2020

Asalin hoton, Reuters
Fitaccen mawaƙin nan na Amurka Kanye West ya ƙaddamar da yaƙin neman zaben ƙasar na 2020, a wani yanayi na ba kasafai ba a garin Charleston da ke jihar South Carolina.
West, mai shekara 43, ya tsaya takara ne a jam'iyyar da ya kafa mai suna "Birthday Party".
A wajen yaƙin neman zaben, da alama mawakin bai damu da yin jawabi kan tsare-tsarensa ba inda ya yi ta iface-iface kan batutuwa da dama, ciki har da batun zubar da ciki da kuma mai fafutukar zubar da ciki Harriet Tubman.
Magoya bayansa na ganin ya ƙaddamar da yakin neman zaben ne kawai a wannan looaci domin ya tallata wakokinsa.
Taron yaƙin neman zaben na Charleston bai kawar da zargin da wasu suke yi cewa ba da gaske yake neman shugabancin Amurka ba.
Kazalika wani saƙon Twitter da aka wallafa a shafin na West wanda daga bisani aka goge, ya nuna jerin wakokinsa kuma ya ƙara rade radin da ake yi cewa ba da gaske yake takara ba.
A taron, wanda aka gudanar a wani wajen da ake gudanar da tarukan biki, an bar mutanen da suka yi rijista kaɗai ne suka halarce shi - ko da yake shafin intanet na yakin neman zaben West ba ya ɗauke da wata alama da ke bai wa mutane damar yin rijista.
Me Kanye West ya ce a wurin yaƙin neman zaben?
West ya yi askin da aka rubuta "2020" kuma yana sanye da tufafi masu sulke, kuma ya yi jawabi ne ba tare da amsa kuwwa ba.
Kazalika mahalarta taron ba su yi amfani da amsa kuwwa ba, abin da ya sa West ya rika nanata musu cewa su yi shiru domin ya ji tambayoyin da ake yi masa.

Asalin hoton, Reuters
A wasu lokutan da yake jawabi ya riƙa kuka musamman da yake magana a kan zubar da ciki, yana mai cewa iyayensa sun kusa zubar da cikinsa: "Watakila da ba a haifi Kanye West ba, saboda mahaifina mutum ne da abubuwa suka sha masa kai."
Ya ƙara da cewa: "Na kusa kashe 'yata... ko da a ce matata [Kim Kardashian West] za ta sake ni bayan wannan kalami, ita ta haifi North a lokacin da ba na son hakan."
Sai dai ya ƙara da cewa ya yi amannar ya kamata a ci gaba da zubar da ciki, ko da yake yana ganin ya kamata a rika bai wa matan da ke fama da irin wannan ciki tallafin kuɗi - yana mai cewa "ya kamata a bai wa dukkan wanda ke cikin wannan hali miliyoyin dala".
"Abin da kawai zai sa mu tsaira shi ne mu rika bin dokar da aka sanya," a cewarsa. "Ya kamata a halasta zubar da ciki saboda me? Saboda ba ubangiji ne ya yi wadannan dokoki ba, don haka me ya sa ake maganar halasci?"

Asalin hoton, Getty Images











