Coronavirus a Najeriya: Ɗaliban Najeriya sun gaji da zaman gida

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Da alama ɗaliban Najeriya sun gaji da zama a gida bayan wata kusan huɗu da rufe makarantunsu a ƙasar da zummar ɗakile yaɗuwar annobar cutar korona.

Tun 26 ga watan Maris Gwamnatin Tarayya ta rufe dukkan makarantun ƙasar, matakin da ya shafi makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.

Sai dai a farkon watan Yuli gwamnati ta ce ɗaliban sakandare na shekarar ƙarshe za su koma azuzuwansu amma ba lallai ne hakan ta samu ba kasancewar gwamnatin ta ce ba za a rubuta jarrabawar WAEC ba ta 2020.

A ranar Juma'a matasan kasar suka kaddamar da maudu'in #SaveNigerianStudents wato "a ceci ɗaliban Najeriya" inda aka yi ta amfani da shi wajen bayyana abin da ke ransu fiye da sau 4,160 a shafin Twitter, inda da dama suke kira da a buɗe makarantun kamar yadda aka buɗe sauran harkoki.

Ga dai wasu daga cikin irin kiraye-kirayen da matasan ke yi:

Naheem ya ce: Abin kunya ne a buɗe harkokin zaɓe da na addini amma a ce har yanzu cibiyoyin gina ƙasa na kulle."

A wasu jihohin Najeriyar, an riƙa koyar da wasu darusa ta hanyar intanet, wasu kuma ta talabijn, wanda ana iya cewa ƙoƙari ne da aka yi domin cike wagegen giɓin da ya bayyana sakamakon rufe makarantun.

Wani mai suna @Itz_Reason10 ya wallafa bidiyon wata 'yar ƙaramar yarinya tana cewa "ni ɗin nan da kuke gani na gaji da zaman gida, don Allah ku bude mana makarantun nan".

Olaniyi ya ce: Idan za a buɗe kasuwa, a buɗe coci, a buɗe kamfe na siyasa, sannan a yi zaɓe, babu abin da zai hana buɗe makarantu."

Ya zuwa yanzu, babu jihar da ta ce za ta buɗe makarantu a kasar, yayin da suke jiran Gwamnatin Tarayya ta ba su tsarin yadda buɗe makarantun zai kasance.

A cikin watan Yuni ma an yi ta rade-radin cewa gwamnatin jihar Kano za ta bude makarantu, sai dai ta musanta batun cewa za ta fara shirye-shiryen bude makarantun, sabanin rahotannin da wasu kafofin watsa labarai suka bayar cewa ta kafa wani kwamiti domin nazari kan sake bude su.

Kasashen duniya da dama musamman a Turai sun bude makarantunsu, amma har yanzu akwai wadanda ba su shirya budewa ba.

A Afrika ma kasashe kamar Nijar da Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya sun bude makarantunsu, sannan Ghana ba ta taba rufe nata makarantun ba tun farkon bullar cutar.

Yaushe Najeriyar za ta bude makarantun?

Wannan tambaya ce da babu wanda ke da amsarta, musamman ganin cewa ko a baya-bayan nan gwamnatin ta sanar da dakatar da zana jarrabawar WAEc ta 'yan ajin karshe na sakandare, bayan da tun da fari ta saka ranar.

A yanzu a iya cewa ko 'yan ajin karshen ba su san takamaimai halin da suke ciki ba na kammalawa a bana.

Sannan a ranar 6 ga watan Yuni gwamnatin Najeriyar ta ce ba ta tsayar da ranar bude makarantun ba wadanda aka rufe sakamakon annobar cutar korona.

Ministan lafiya na kasar ne Dr Osagie Ehanire ne ya bayyana haka a taron manema labarai ranar Asabar da aka cika kwanaki 100 da bullar cutar korona a Najeriya.

Gwamnatin ta ce za ta ci gaba da duba yiyuwar bude makarantun ta la'akari da bin matakai na hana kara yaduwar cutar a kasar.

Ministan ya yi kira ga makarantu su rungumi tsarin koyarwa a Intanet har zuwa lokacin da za a bude makarantun. Sai dai wannan wani abu ne da iyaye da dama ke kokawa akai musamman ganin cewa abu ne da ke bukatar sayen data don hawa intanet da kuma mallakar wayar da za ta iya yin hakan ko kuma komfuta.

Ministan lafiyar a lokacin ya ce za a bude makarantun ne kawai idan hatsarin bazuwar cutar ya ragu. Amma ga dukkan alamu yawan masu cutar karuwa yake kullum a anJAeriya maimakon raguwa.