Fahim Saleh: Rayuwar shugaban Gokada cikin hotuna a Najeriya

Asalin hoton, Instagram/ fahims
- Marubuci, Olaronke Alo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist, BBC Pidgin, Lagos
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 2
Kafin 'yan sandan New York su gano gawar Fahim Saleh da aka daddatsa a cikin wani gida na unguwar hamshaƙai ta Manhattan, shugaban kamfanin Gokadan ɗan shekara 33 ya sha zuwa Najeriya inda yake kai ziyara cibiyoyin ƙirƙirar fasahohin zamani.
Sai dai a ranar Talata 14 ga watan Yuli, mummunan labari ya riski al'ummar ƙasar cewa an kashe Fahim Saleh a gidansa inda kuma aka sa zarto mai amfani da lantarki aka yi gunduwa-gunduwa da gawarsa.
Yanzu, 'yan sandan birnin New York na gudanar da bincike kan abin da suke jin mai yiwuwa kisan kai ne, bayan mummunan kisan gillar da aka yi wa Fahim Saleh.
Sai dai kafin duk wannan balahira, zai yi kyau mu yi nazari game da alherinsa
Fahim Saleh a wasu lokutan farin ciki sa'ar da yake Najeriya

Asalin hoton, Instagram/ Fahim Saleh

Asalin hoton, Instagram/ Fahim Saleh

Asalin hoton, Instagram/ Fahim Saleh

Asalin hoton, Instagram/ Fahim Saleh

Asalin hoton, Instagram/ Fahim Saleh

Asalin hoton, Instagram/ Fahim Saleh

Asalin hoton, Instagram/ Fahim Saleh
Bayan gwamnatin jihar Lagos ta hana amfani da baburan haya waɗanda aka fi sani da Okada, hakan ya shafi harkokin kasuwancin Fahim Saleh a Najeriya.
Shugaban kamfanin Gokadan cikin wani yanayi na kusa ƙwalla, ya wallafa wani bidiyonsa na ƙarshe a shafin Instagram a watan Fabrairu yana roƙon gwamnatin jihar Lagos ta sakar wa masu sana'ar fasahohin sadarwa mara a jihar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram

Asalin hoton, Twitter/ Fahim Saleh





