Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tunisia: An ɗaure wata mata saboda ta yi rubutu cikin salon ayar Kur'ani a Facebook
An ɗaure wata mata a ƙasar Tunisia mai wallafa bayanai a intanet tsawon wata shida a gidan yari bayan ta wallafa wani saƙo kan cutar korona ta hanyar kwaikwayon salon wata ayar Ƙur'ani.
An kama Emna Charqui mai shekara 28 a watan Mayu bayan ta wallafa saƙo a Facebook tana mai shawartar mutane da su bi hanyoyin kariya cikin salon ayar Kur'ani - littafi mai tsarki kuma mafi girma ga Musulmai.
Charqui ta bayyana a wata hira ta baya-bayan nan cewa ba ta yi niyyar tsokanar kowa ba amma saƙon da ta wallafa ya birge ta.
Wata kotu ta same ta da laifin "haifar da ƙiyayya tsakanin addinai".
Zuwa yanzu ba a garƙame ta a gidan yarin ba sakamakon aniyarta ta ɗaukaka ƙara.
A ranar 2 ga watan Mayu, Charqui ta yaɗa wani saƙo a shafinta na zumunta tana kwaikwayon ayar Kur'ani. A ciki ne kuma ta yi kira ga mutane da su riƙa wanke hannu da kuma yin nesa-nesa da juna domin kauce wa kamuwa da cutar korona.
An ruwaito cewa wani maras addini ne ɗan Algeria da ke zaune a Faransa ya fara saka hoton.
Charqui ta wallafa nata saƙon ne a watan Ramadana, yayin da ƙasar Tunisia ke tsaka da dokar kulle.
Ta tayar da ƙura a shafukan sada zumunta, inda har wasu suka yi kiran da a hukunta Charqui, wadda ita ma ba ta bin kowanne addini.