Hukumar Neja-Delta ta bayyana yadda ta raba wa ma'aikatanta N1.5bn na tallafin korona

Asalin hoton, Twitter/NDDC
Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ta bayyana wa wani kwamitin majalisar dattawan Najeriya da ke binciken ta dalilan da suka sa ta raba wa manyan shugabanni da ma'aikatan hukumar ta NDDC naira biliyan 1.5.
Yayin wani zama da aka yi a majalisar kasa da ke Abuja, shugaban kwamitin, Sanata Olubunmi Adetunmbi ya bayyana yadda aka raba kudaden:
- An bai wa wani ma'aikaci naira miliyan 10 a matsayin "tallafi"
- Hukumar NDDC ta raba wa wasu ma'aikata biyu naira miliyan 14
- Ma'aikata uku kuma sun karbi naira miliya biyar-biyar
- Ma'aikata 148 an ba su naira miliyan uku-uku
- Ma'aikata 157 sun karbi naira miliyan daya da rabi-rabi
- Wasu ma'aikatan 497 sun karbi naira miliyan daya kowannensu
- Ma'aikatan da ba su sami kudi sosai ba su ne masu shara, wadanda aka mika naira 600,000 ga kowannensu, kuma ya ce sun kai su 464
- NDDC ta raba wa 'ƴan sanda naira miliyan 475 cikin kuɗin "domin su sayi takunkumi da sinadarin tsaftace hannu".
Sanatan ya kuma ce cikin naira biliyan 3.14 da aka ba NDDC domin annobar Covid-19, hukumar ta raba wa ma'aikatanta naira biliyan 1.5 a matsayin tallafin cutar korona.

Mene ne bayanin NDDC kan rabon kudin da ta yi?
Shugaban riko na hukumar NDDC Kemebradikumo Pondei ya bayyana cewa:
"Tun farko shigowar Covid-19 muka dauki matakin bayar da tallafi ganin cewa aikin NDDC ne ta bayar da tallafi".
Ya kuma ce, "muna da kalubalen da suka sa muka bayar da tallafin naira miliyan 775 ga jihohi tara."
"Kuma bayan wannan akwai wasu naira miliyan 170 na daban. Muna da mazabun sanatoci 27 a NDDC kuma saboda matsin da muke samu daga masu ruwa da tsaki a yankinmu, sai muka kasafta kuma muka sami amincewar rabawa kungiyoyin matasa kana muka ba kungiyoyin mata naira miliyan biyar su ma.
"Akwai kuma masu naƙasa a kowace mazabar sanata daga jihohi tara da kudinsu ya kai naira miliyan 270, kamar yadda ya fada."
Game da ma'aikatan hukumar, ya ce: "NDDC na da ma'aikata fiye da 4,000 a jihohi tara na kudancin kasar nan, kuma kowannensu tamkar wakilcin jama'arsa yake. Mun fuskanci matsi sosai kan batun, shi ya sa muka biya kudaden.
"Mun yi haka ne domin rage tasirin annobar kan matasa tun da ba sa aikin komai. Mun bayar da tallafin ne domin kauce wa tashin hankali," in ji shi.

A kan dalilin da hukumar ta raba wa ƴan sanda naira miliya 475 kuwa, Mista Pondei ya ce: "Mun sami wani sako ne daga babbar shalkwatar ƴan sanda, kuma shugabannin NDDC sun duba sakon sun amince da a taimaka mu su da kudin."
A watan Mayun 2020 ne majalisar dattawan Najeriya ta nada kwamitin mutum bakwai domin ya binciki dalilan da shugabannin riko na NDDC suke facaka da kudaden al'umma tsakanin 29 ga watan Oktoban 2019 zuwa 31 ga watan Mayun 2020.

Asalin hoton, Twitter/Senate
Sauran abubuwan da aka gano yayin zaman da aka yi na binciken NDDC
Daya daga cikin mambobin kwamitin binciken, Sanata Betty Apiafi ta ce ayyukan da NDDC ke yi ba sa karewa, inda ta ce akan taras da ayyukan a cikin kasafin kudi na NDDC har tsawon shekara 15 zuwa 20.
Shugaban kwamitin, Sanata Adetunmbi ya ce hukumar gudanarwa ta NDDC ta kashe naira biliyan 81.5 cikin wata takwas, kamar yadda takardun da hukumar ta mika wa kwamitin suke cewa.
Jadawalin dukkan kuɗaɗen da NDDC ta kashe cikin watannin da ake bincikenta
Za a ci gaba da zaman kwamitin a yau inda za a gayyaci kungiyar masu kwangila ta Neja Delta da sauran kungiyoyi masu rajin kare hakkokin bil Adama domin su mika nayanansu.












