Coronavirus: Cutar tana yaɗuwa ta iska - WHO

Asalin hoton, AFP
A karon farko, Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince cewa cutar korona na iya yaduwa a iska.
Hukumar na martani ne game da wata budaddiyar wasika da ta fito daga masana kimiyya sama da dari biyu da suka bukaci ta sabunta shirinta.
A baya dai WHO ta dage kan cewa cutar na yaduwa ne sanadiyyar wasu kananan kwayoyi dakan fito daga hanci ko bakin wadanda suka kamu.
Daya daga cikin masana kimiyyar da suka aike da wasikar shi ne Joe Allen na Jami'ar Harvard.
Ya ce hujjujojin da muka samu na kimiyya a fayyace suke, wannan batu na cewa cutar na yaduwa a iska na faruwa, shi ya sa muka ankarar da hukumar da baki daya.
Idan aka tabbatar da wannan batu, zai ya shafar ka'idodjin kariya da aka sanya game da m'amala a ckin gidaje da ofisoshi da makamantansu.
Wasikar da masana kimiyyar suka rubuta ta zargi WHO da raina shaidar da ta nuna yiwuwar daukar cutar korona ta iska.
WHO ta ce ya zuwa yanzu ana dakar cutar ne ta hanyar tari ko atishawa da makamantasu.
Masanin magunguna Jose Jimenez na Jami'ar Colorado, daya daga cikin masaan da suka rubuta wasikar, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa: "Da ma so muke su [jami'an WHO] su yarda da wannan shaida.
"Tabbas hakan ba suka ba ce ga WHO. Tataunawa ce ta kimiyya, ko da yake muna ganin ya kamata mu fada wa duniya saboda mun ga sun ki amincewa da shaidun da muka gabatar musu a tattaunawar da muka yi da su," in ji shi.

Sauya matsayi?
Sharhi daga Imogen Foulkes, BBC News a Geneva
WHO ta kwashe wata da watanni tana dagewa cewa cutar korona tana yaduwa ne idan mutum ya yi tari ko atishawa sannan wani ya shafe su. Ruwan da ke fita daga tari o atishawa ba ya dadea a cikin iska yake saka kasa - si ya sa aka bayar da shawara ga mutane su rika wanke hannayensu.
Sai dai masana kimiyya 239 daga kasashe 32 sun ce ba haka batun yake ba: sun ce akwai kwakkwarar shaida da ke nuna cewa cutar tana yaduwa ta iska: ta hanyar burbushin wasu abubuwa da ke yawo cikin iska tsawon sa'o'i bayan mutane sun yi magana ko numfashi.
Yau WHO ta amince cewa cutar tanayaduwa ta iska a wasu wurare, irin su wuraren da ke kulle ko wanda ke ciki makil da jama'a.












