Coronavirus a Najeriya: Tarin mai korona nawa za ka shaka ka harbu?

DR GWARZO
Bayanan hoto, Dr. Sani Gwarzo
An wallafa

Ƙwararru kan cututtuka masu yaduwa sun yi gargadi kan yadda kwayoyin cutuka ke saurin yaduwa a cikin al'umma yayin da ake fargabar sake bullar cutar korona a karo na biyu.

A tattaunawarsa da BBC Dokta Sani Gwarzo wanda kwararre ne kan cutuka masu yaduwa, ya ce akwai bukatar mutane su ci gaba da amfani da gargadi da kuma daukar matakan kare kansu daga kamuwa da korona.

Dokta Gwarzo ya ce wani bincike da aka gudanar kan yaduwar cututtuka ya nuna cewa a duk lokacin da mutum zai bude bakinsa to ana samun fitar kananan kwayoyin cutuka 200 a kowanne minti guda.

Sannan ya ce idan aka yi atishawa kwayoyin kananan cututtuka miliyan 200 ake fitarwa, a kowanne numfashi kuma ana fitar da kwayar cuta 20.

Wannan layi ne
Wannan layi ne

''Kuma cikin miliyan 200 nan idan mutum na zaune kusa da kai ba tare da ya sanya takunkumi ko mai tarin na sanye da takunkumi ba, akalla zai yada cutuka dubu cikin abin da ya fitar.

''Yayin da mutum ya yi magana, kowane buda baki na tafe da kwayoyin cutuka, ka ga ashe akwai mumunan hadarin kamuwa da cutaka idan ba a yi hattara ba.''

Dokta Gwarzo ya ce an gano hakan ne a wani sabon binciken da aka yi kwana nan kan saurin yaduwar cutukar korona.

Cutar korona dai na ci gaba da karuwa a Najeriya inda yanzu akwai akwai mutum sama da dubu 26 da suka kamu da cutar, kuma har yanzu jihar Legas ke kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar.

Masana dai na ci gaba da bayyana fargaba da kuma ankarar da mutane kan amfani da bin shawarwari wajen kare kai daga kamuwa da korona.