Yadda aka ceto ‘yar Philippine daga hannun wani dan damfara a Najeriya

NPF

Asalin hoton, NPF

Bayanan hoto, Ko a lokacin da `yan sanda suka cece ta, sun same ta a halin rashin lafiya, don haka ne ba su ɓata lokaci ba suka wuce da ita asibiti
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar `yan sandan Njaeriya ta ce ta yi nasarar ceto wata mata `yar kasar Philippines daga hannun wani dan Najeriya da ake zargin mayaudari ne.

Wanda ya tsare ta a gidansa na tsawon watanni, bayan ta kai masa ziyara da sunan soyayya.

Rundunar `yan sandan reshen jihar Enugu ta yi nasarar ceto ta ne, bayan an tsegunta ma ta inda aka kulle ta.

Matar `yan kasar Philippines mai suna Irene Torento Panas, `yan shekara 40 da haihuwa ta daka-gari ne daga kasarta zuwa kauyen Neke-Uno da ke karamar hukumar Enugu ta gabas, da ke jihar Enugu, a kudu-maso-gabashin Najeriya.

Ta kuma je ne da zummar rai zai ga rai, wato za ta yi tozali da masoyinta. Chukwudi Odo, dan shekara 54, bayan sun kulla abotarsu ta shekara biyu ta dandalin sada zumunta na facebook, inda suka yi ta yin zancensu ta hanyar tura wa juna sakonni, wato tun a ranar 8 ga wata Maris na 2017, ashe ashe…rabon wahala… Irene Torento Panas ta dauki kara da kiyashi!

Cikin wata sanarwa, Kakakin rundunar `yan sandan Najeriya, Frank Mba ya ce Irene Torento dai ta amsa gayyatar abokin nata ne cewa za ta kai masa ziyarar kwana goma a gidansa a Najeriya, kuma ta isa Najeriyar a ranar 22 Ga Watan Nuwamban bara, amma tana isa sai ya garƙame mata kofa ya hana ta komawa kasarsu, sannan ya datse duk wata hanyar da za ta yi magana da `yan uwanta.

Haka ta zauna har tsawon wata shida ba ta jin duniyar `yan uwanta. Su ma ba sa jin tata duriyar.

Binciken da `yan sanda suka yi ya gano cewa da niyya masoyi ko mayaudarin nata, wato Chukudi Odo ya yi wa buduwar ta sa shigo-shigo-ba-zurfi domin ya ci zarafinta a zaman da suka yi ta hanyoyi da dama, ciki har da lalata da ita, da kuma damfararta, ko cinye mata wasu `yan kudadenta.

Ko a lokacin da `yan sanda suka cece ta, sun same ta a halin rashin lafiya, don haka ne ba su ɓata lokaci ba suka wuce da ita asibiti.

Su ma `yan sandan, kamar yadda kakakinsu yake cewa wasu mutanen kauyen Neke-Uno din ne suka tsegunta musu wurin da ake boye matar, kana suka kai samame, suka kubutar da ita.

A halin da ake ciki dai, rundunar `yan sandan ta ce ta tuntubi ofishin jakadancin kasar Philippines da ke Najeriya da nufin bin matakan hada matar da `yan uwanta.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Babban sufetan 'yan sandan Najeriyar Muhammad Adamu ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin rundunar na tuwita ya shawarci masu amfani da kafafen sada zumunta da su zama masu takatsantsan da wadnda suke mu'mala da su.