Godwin Obaseki: PDP ta amince gwamnan Edo ya shiga zaben fitar da gwani

An wallafa

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta amince gwamnan jihar Edo Godwin Obasaki wanda ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki da ya tsaya takarar a zaben fitar da gwani da zai gudana nan gaba.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, PDP ta ce la'akari da tanade-tanaden kundin tsarin mulkinta, Gwamna Obasaki na da damar tsayawa takarar fitar da gwani a zaben gwamna na jihar.

Haka zalika kwamitin koli na PDP wanda shi ne ke kan gaba wajen tabbatar da bin tsarin jam'iyyar ya ce mataimakin gwamnan Philip Shu'aibu shi ma na da damar shiga a dama da shi wajen zaben zama mataimakin gwamnan.

Kwamtin ya sanar da matsar da zaben fitar da gwanin na gwamnan jihar Edo da aka fara tsarawa zai gudana ranar Talata 23 ga watan Yunin da muke ciki zuwa ranar Alhamis 25 ga watan.

A makon jiya ne kwamitin tantance masu neman takarar gwamna na jam`iyyar APC a jihar Edo ya tabbatar da cire Gwamna Godwin Obaseki daga cikin waɗanda za su yi takarar.

Gwamnan ya ce ya shiga PDP domin "na samu cimma burina na sake lashe zaben gwamnan jihar Edo."