Marcus Rashford da wasu 'yan Gasar Premier da ke kawo sauyi a al'umma

Troy Deeney, Marcus Rashford and Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

A ranar Talata, Marcus Rashford ya nemi a tallafa wa yara miliyan 1.3 domin samun abinci kyauta a lokacin wannan bazarar.

Tuni dan wasan na Manchester ya tara fam miliyan 20 domin kai abinci ga marasa ƙarfi a lokacin wannan annobar.

Martani mai daɗi da jama'a ke mayarwa kan irin nasarar da ɗan kwallon ya samu ya sauya tunanin jama'a da dama kan yadda ake kallon 'yan kwallo.

Kuma Rashford mai shekaru 22, ba shi kaɗai yake amfani da sana'arsa ta taka leda ba domin taimako.

Troy Deeney

Asalin hoton, PA Media

Troy Deeney

Kyaftin din Ƙungiyar Watford Troy Deeney yana cikin waɗanda suka yi fice - ba wai don kawai ya taimaka wa ƙungiyar samun ƙarin girma ba shekaru biyar da suka wuce, amma ya sauya rayuwarsa a matsayin wanda ya fi cin kwallaye

Ɗan kwallon mai shekara 31 ya taɓa shiga gidan kurkuku a 2012, a halin yanzu yana da gidauniyar tallafa wa marasa ƙarfi tare da matarsa Stacey.

An kafa ƙungiyar ne domin ta samar da kuɗaɗe ga yara masu naƙasa da ke makaranta. Ƙungiyar a halin yanzu tana tara kuɗi don gina wata cibiya ta wasanni sakamakon wata makaranta ta masu naƙasa da ke kusa da gidan dan ƙwallon a Watford.

Raheem Sterling

Sterling na ɗaya daga cikin manyan ƙadarorin da Manchester ta mallaka a cikin filin kwallo, amma ba ita kaɗai ta mallake shi ba.

A makon da ya gabata, ya fito a cikin shirin Newsnight inda aka tattauna da shi kan batun nuna wariyar launin fata a Birtaniya kuma ya kwarzanta maudu'in nan da ake ta magana a kai na Black Lives Matter, wato rayuwar baƙar fata na da amfani, zanga-zangar da ake yi a faɗin Birtaniya.

Sterling mai shekaru 25, an san shi da taimakon marasa galihu - kuma an haife shi har ya girma a Wembley, da ke Landan.

A shekarar da ta gabata, ya biya wa ɗalibai 500 waɗanda 'yan makarantar da ya taɓa halarta ne domin su je su kalli wasan kusa da na ƙarshe tsakanin Manchester da Brighton.

Ya kuma bayar da gudunmawa da ba a bayyana ko ta nawa ba ce ga waɗanda gobarar Grenfell Tower ta rutsa da su a 2017.

Mo Salah

Asalin hoton, Reuters

Mo Salah

Mo Salah wanda ya ci kyautar wanda ya fi cin ƙwallaye a Gasar Zakarun Turai, an san shi da kyauta.

Ƙungiyar da ya kafa na taimakon gidaje 450 a ƙauyen da ya fito a Basyoun da ke Masar inda a duk wata ya ke ba su alawus.

Yana kuma taimaka wa da kuɗi domin taimaka wa 'yan ƙwallo masu tasowa a nan Ingila.

Juan Mata

Juan Mata wanda ɗan Manchester ne, ba wai yana bayar da gudunmawa ga marasa ƙarfi ba kawai, amma yana ƙarfafa gwiwar manyan 'yan wasa su bayar da tallafin su ma.

Ɗan wasan gaban Sifaniyar ya kafa wata gidauniya da ake kira Common Goal a 2017 inda 'yan wasa da koci-koci na ƙungiyoyi ke bayar da gudunmawar kashi ɗaya cikin 100 na abin da suke samu a duk wata ga ƙungiyoyin tallafi na ƙwallo faɗin duniya.

Tsarin da ya ɗauko na da sama da mambobi 470, ciki har da kocin Liverpool Jurgen da kuma wadda ta lashe gasar Ballon D'Or a rukunin mata wato Megan Rapinoe.

Arsenal's Mesut Ozil

Asalin hoton, Getty Images

Mesut Ozil

Duk da cewa ɗan wasan bai taka wata rawar gani ba a wannan kakar wasan ta bana, amma duk da haka Ozil na nan yana taimako yayin da aka dakatar da ƙwallo a wannan lokaci na ƙulle.

Ya bayar da gudunmawar fam 80,000 ga Musulmai a Turkiyya lokacin watan Ramadana da ya gabata.

Ɗan wasan wanda ke buga wa Jamus duk da cewa ɗan asalin Turkiyya ne, ya bayar da taimakon ga mutum 16,000 waɗanda ke cikin wani hali.

Ko a lokacin bazarar bara da ya yi aure, ya ƙi amsar kyaututtukan da ak kawo masa inda ya gwammace ya biya wa yara 1,000 kuɗin asibiti.

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

line