Koriya Ta Arewa za ta tura dakaru kan iyakarta da Kudu

An wallafa

Ministan tabbatar da hadin kai na Koriya Ta Kudu ya yi murabus sakamakon tashe-tashen hankulan da ake kara samu tsakanin kasarsa da Koriya Ta Arewa.

Kim Yeon-chul ya ce ya dauki alhakin tabarbarewar dangantaka tsakanin kasashen na Koriya biyu.

Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Talata Koriya Ta Arewa ta tarwatsa wani ofishin hadaka tsakaninta da Koriya Ta Kudu, wanda aka gina da zummar inganta dangantaka tsakanin su.

Rundunar sojin Koriya Ta Arewa ta ce za ta tura dakarunta kan iyaka.

A ranar Laraba ne Korita Ta Arewa ta yi karin haske kan dalilin da ya sa ta tarwatsa ofishin da ke Kaesong.

Wata makala da kafar yada labarai ta kasar ta fitar ta zargi Koriya Ta Kudu da karya yarjejeniyoyin da aka kulla a shekarar 2018 tana kuma nuna halayyar - yayin da 'yar uwar Shugaba Kim Jong-un kuma ta zargi shugaban Koriya Ta Kudu da zama dan koren Amurka.

Koriya ta Kudu dai ta ce a shirye take a sasanta, amma kuma ta yi Allah-wadai da matakan ''rashin hankali'' da Arewar ke dauka.

Tashin hankali na ta karuwa a makonnin baya-bayan nan - sakamakon tura sakonnin da masu farfaganda 'yan Arewa da suka tsere Kudu ke aikawa kan iyakar Arewan.

Me Arewa ta ce?

Kafafen yada labaran Koriya Ta Arewa sun zargi Kudu da karya da lalata yarjejeniyar da aka cimma a 2018, da suka hada da Panmunjom Declaration.

Makalar ta ce ma'aikatar tsaron Koriya Ta Kudu ba ta da alkibla.

Ta kuma rufe da yin gargadi da cewa tarwatsa ofishin tuntuba da ta yi jiya somin tabi ne na lalacewar da dangantakar kasashen biyu za ta yi.

Kazalika Arewa ta ce za ta tura dakaru zuwa wasu wurare biyu hadin kan Koriya a baya, da rufe masana'antar hadin gwiwa da ke Kaesong da kuma wajen yawon bude ido na Tsibirin Kumgang da ke gabar teku.

Sannan kanwar Shugaba Kim-Jong-un na takalar Shugaba Moon Jae-in na Kuud.

Wane martani Kudu ta mayar?

Ofishin shugaban Koriya Ta Kudu a ranar Laraba ya ce abin da Arewa ta yi rashin hankali ne - ya kuma yi gargadi cewa kasarsa ba za ta sake daukar dabi'ar rainin hankali daga Arewa ba.

Duk da tarwatsa ofishin tuntubar da ka yi, Kudu ta ce tana fatan za a girmama yarjejniyar da aka cimma a 2018.