Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Breonna Taylor: Beyoncé ta nemi a yi adalci kan kisan bakar fata
Fitacciyar mawakiyar Amurka Beyoncé ta bukaci a yi adalci kan kisan da 'yan sanda suka yi wa wata mace bakar fata a wasikar da ta aike wa antoni janar na jihar Kentucky.
Mawakiyar ta nemi Anto Janar na Kentucky Daniel Cameron ya tuhumi 'yan sanda uku da ke da hannu a kisan Breonna Taylor.
'Yan sandan sun harbi Ms Taylor, mai shekara 26, sau takwas lokacin tana bacci a dakinta yayin da 'yan sandan suka shiga gidansu da ke Louisville ranar 13 ga watan Maris.
Sun je gidan ne domin yin samame kan zargin da aka yi cewa an boye miyagun kwayoyi a cikinsa, lamarin da aka gano babu kanshin gaskiya a cikinsa.
Lokacin da suka shiga gidan, sun yi musayar wuta da saurayin Ms Taylor, wanda ya yi zaton barayi ne suka shiga gidan.
Ƴan sanda sun ce sai da suka ƙwanƙwasa kafin daga bisani su yi amfani da wani ƙarfe don bude ƙofar suka shiga gidan, amma iyalan Ms Taylor da wani maƙwabcinsu sun ƙaryata wannan bayanin.
An dakatar da 'yan sandan uku da ke da hannu a lamarin Jon Mattingly, Myles Cosgrove, da kuma Brett Hankison na dan lokaci amma babu wanda aka kama ko ake tuhuma da kisan Ms Taylor. Ana dai ci gaba da bincike.
''Wata uku sun wuce kuma har yanzu iyalan Breonna Taylor na jiran hukuncin da za a yanke,'' kamar yadda Beyoncé ta rubuta a wasikar, wacce aka wallafa a shafinta na intanet ranar Lahadi.
An sake tayar da batun kisan Ms Taylor ne bayan kashe wani bakar fata dan Amurka George Floyd, da dan sanda farar fata ya yi a Minneapolis da ke Minnesota a watan da ya gabata.
An yi amfani da sunan Ms Taylor a zanga-zangar adawa da kisan bakaken fata da aka yi ta yi a Amurka da wasu sassan duniya.