George Floyd: 'Yan sanda sun sake kashe wani bakar fatan Amurka a Atlanta

An wallafa

Shugabar 'yan sandan birnin Atlanta ta ajiye aikinta bayan da wasu 'yan sanda suka harbe wani bakar fata har lahira.

Erika Shields ta ajiye mukaminta ne bayan da hotunan bidiyo da masu wucewa suka nada, inda suka nuna yadda rikici ya kaure tsakanin 'yan sandan da wani bakar fata da yake zaune cikin motarsa a wani gidan sayar da abinci.

Masu zanga-zanga sun cika titunan birnin jim kadan bayan da labarai suka fito game da kisan.

'Yan sandan birnin Atlanta sun ce mutumin mai suna Rayshard Brooks mai shekara 27 na barci ne a cikin motarsa yayin da yake jira a kan layin sayar da abincin tafi da gidanka.

Wasu 'yan sanda farar fata sun harbe shi bayan da rikici ya barke tsakaninsu da shi saboda ya ki amincewa su tafi da shi ofishinsu domin sun ce wai da alama a buge yake da giya.

Darkatan ofishin bincike na jihar Georgia ya ce kyamarorin da ke cikin gidan abincin sun nuna MIsta Rayshard na gudu da makamin Taser mallakin daya daga cikin 'yan sandan a hannunsa.

Yayin da ta ke sanar da ajiye aikin shugaba 'yan sandan, Keisha Lance Bottoms - wadda ita ce Magajiyar Garin Atlanta ta ce tilas 'yan sanda su nemi sake kulla dangantaka tsakaninsu da al'umomin da suka rantse za su kare su, a maimakon a rika jin labarai irin wannan masu cike da takaici.

Masu zanga-zanga sun taru a wurin da aka kashe Mista Brooks da kuma wasu sassa na birni domin nuna bacin ransu, wanda ke zuwa kusan mako uku da kisa George Floyd a birnin MInneapolis - kisan da ya haifar da zanga-zangar da ba a taba ganin irinta ba a tarihin Amurka.