Ƙayatattun hotunan Afirka na makon nan daga 29 ga Mayu - 4 ga Yunin 2020

An wallafa

Zaɓaɓɓun hotunan makon nan kuma ƙayatattu daga Nahiyar Afirka:

Kenyan photographer and art director Barbara Minishi (L) takes pictures of her room mate and fashion stylist Wambui Thimba (R)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bayan an gaza gudanar da bikin tallar tufafi saboda annobar korona, masu tallar sun gudanar da bikin a saman rufin gidajensu a babban birnin Kenya, Nairobi.
A young Fulani herder sits on his donkey in the village of Mbetiou Peulh on May 29, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan makiyayin shi ma rayuwarsa na cikin wani hali sakamakon annobar tun daga watan Maris. Ga shi nan zaune a kan jakinsa ranar Juma'a a ƙauyen Mbetiou Peulh na ƙasar Senegal.
A student washes her hands as they attend their first day of re-opened school in Dar es Salaam, Tanzania, on June 1, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu ɗalibai sun koma makaranta ranar Litinin a ƙasar Tanzania...
Students attend a class on their first day of re-opened school in Dar es Salaam, Tanzania, on June 1, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, .... sai dai ɗaliban jami'a ne kawai suka koma azuzuwa, da kuma na kwaleji, sai kuma 'yan shekarar ƙarshe a sakandare.
A child in Johannesburg has his temperature measured as he enters the school premises on June 1, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Litinin ɗin dai, wani mutum yana gwada zafin jikin wani yaro a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
A pupil wearing a face mask as a preventive measure against the spread of the COVID-19 coronavirus writes on the blackboard in Yaoundé, Cameroon, 1st June 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Kamaru ma, ranar Litinin aka koma makarantu.
South African National Defence Force (SANDF) soldiers patrol among street vendors and food stalls at the Bara taxi rank in Soweto, Johannesburg, on June 1, 2020,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An ƙyale dukkanin harkokin kasuwanci su ci gaba a Afirka ta Kudu ban da masu haɗari sosai.
A Sudanese protester clad in mask and latex gloves runs during a demonstration in the Riyadh district in the east of the capital Khartoum on June 3, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mai zanga-zanga kenan a birnin Khartoum na Sudan a ranar Laraba da ke neman a yi wa wasu masu zanga-zangar adalci da aka kashe a shekarar da ta gabata.
A fire in the middle of the street in the Androranga neighbourhood of Toamasina, a large port city on the east coast of Madagascar, on 3 June 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Toamasina na ƙasar Madagascar, mazauna garin sun yi arangama da 'yan sandan kwantar da tarzoma ranar Laraba bayan sun yi wa wani mutum duka da ya karya dokar kulle.
A fighter loyal to the UN-recognised Libyan Government of National Accord (GNA) stands on the high tarmac of Tripoli International Airport following its recapture from rival forces loyal to strongman Khalifa Haftar, on June 3, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kazalika a ranar Larabar, wani mayaƙi na gwamnatin Libya da Majalisar Ɗinkin Duniya ke mara wa baya yana tsaye a filin jirgin saman Tripoli jim kaɗan bayan dakarunta sun ƙwace shi daga hannun dakarun Janar Khalifa Haftar

Hotuna daga AFP, EPA, Reuters.