Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda za ku kula da tarbiyyar yaranku yayin karatu a intanet
Tun bayan da annobar korona ta ɓulla a kasashen duniya, an kulle kusan duka makarantu a duniya a yunƙurin daƙile yaɗuwar wannan cuta. Hakan ya tilasta wa ɗalibai da dama amfani da intanet domin ci gaba da karatu.
Makarantu da dama a faɗin duniya sun fito da tsare-tsare ta yadda ɗalibai za su iya amfani da wayoyin salula ko kuma kwamfuta wajen karatu da kuma yin sauran ayyukan da malamansu kan ba su.
Amma sai dai sakar wa yaran ragamar amfani da intanet ya jawo koma baya ta fannoni da dama a irin wannan lokaci inda akasarin iyaye ke koka wa kan cewa yaran sukan yi amfani da intanet wurin shiga wuraren da ba su kamata ba.
Binciken da masana suka yi ya bayyana cewa tun farko ba a tsara intanet ba ta yadda yara za su yi amfani da ita, sakamakon sauyin zamani da kuma shigowar shafukan sada zumunta ya sa yara ƙanana suka samu damar amfani da intanet.
Haka zalika, na'urorin zamani na da ɗaukar ido musamman ga yara wanda hakan na da wahalar raba su amfani da na'urorin.
Wasu daga cikin iyayen yaran sun shaida wa BBC cewa suna bai wa yaransu wayoyi su yi karatu amma tare da sa ido na iyayen.
Iyayen sun shaida mana cewa sukan tsare yaran a tare da su, kuma su sa musu ido har su gama domin gudun samun wata matsala.
Dangane da wannan batu na sakar wa yara wayoyi da kuma kwamfuta sakaka, BBC ta tattauna da Abdullahi Salihu Baban Saddiq, wani ƙwararre kan harkokin intanet a Najeriya kuma ya bayar da shawarwari biyar kan yadda iyaye za su sa ido ga yaransu masu amfani da intanet.
1- Bibiyar abin da yaro ya ke yi
Abdullahi Salihu ya bayar da shawara ga iyaye kan cewa ya kamata a kullum ya zamana suna bibiyar abubuwan da yaransu suke yi a shafukan intanet.
A cewarsa, akwai hanyoyi da dama ta yadda iyaye za su iya bin diddigi da kuma bibiyar wasu daga cikin abubuwan da yaransu suke yi, idan sun yi hakan, a kalla za su san wane hali yaran ke ciki.
A cewarsa, yana da kyau iyayen yara su san yadda za su buɗe wayoyin yaransu da kuma kwamfutocinsu, ma'ana su san "password" dinsu.
Haka zalika iyayen su rinƙa shiga e-mail din 'ya'yansu domin duba da wa suke hulda kuma ta hakan za su iya sanin wasu shafukan da yaran nasu suka yi rajista da su.
2- Bibiyar abokan yara na shafukan sada zumunta
A halin yanzu, shafukan sada zumunta su ne mafi sauki na yin abokantaka da mutane a faɗin duniya, jama'a daga nahiyoyi daban-daban kan iya yin abota sakamakon yadda intanet ta zagaye duniya.
Ya bayyana cewa "a intanet din mutum zai haɗu da wanda ya sani da wanda bai sani ba da wanda ake ƙasa ɗaya da wanda ba a ƙasa ɗaya ba duk ana haɗuwa".
Masana harkokin intanet na ganin ya kamata iyaye su rinka sa ido kan waɗanne irin abokai yaransu ke hulɗa da su a intanet.
Ana yawan samun masu mugayen ɗabi'u da 'yan kungiyoyin asiri da 'yan zamba cikin aminci ta intanet. Masana na ganin abu ne mai sauƙi a dulmiyar da yara cikin irin waɗannan ɗabi'u.
3- Ilmantar da yara kan munin intanet
A kowane lokaci, masana harkokin intanet na yawan jaddada cewa intanet na da amfani da kuma rashin amfaninta ko kuma muninta. Sanin muninta zai taimaka wa mutum matuƙa wurin sanin yadda zai iya amfani da ita.
Abdullahi Salihu ya bayyana cewa ya kamata iyaye su rinƙa ilmantar da yaransu ko kuma wayar musu da kai kan munin intanet domin sanin illolinta.
Ya ce akwai abin da ake kira intanet "internet black hole", wanda a cewarsa "wuri ne mafi muni a intanet wanda idan mutum ya faɗa ciki ba zai iya fitowa ba, wuraren sun haɗa da wuraren batsa da caca da cuta da sauransu".
Ya ce illolin sabo da shiga irin waɗannan wurare kan yi tasiri ga mutum ƙwarai inda idan aka fara ba za a iya daina wa ba har mutum ya tsufa.
Shawarwari daga bakin iyaye
Dakta Zahra'u Umar, Malamar addini ce kuma kwamishinar harkokin mata ce a jihar Kano ce inda a tattaunawarta da BBC, ta bayar da shawarwari ga iyaye a matsayinta na uwa kan yadda za su rinƙa lura da yaransu yayin da suke amfani da intanet.
A cewarta, a kullum ya kamata iyaye su rinƙa tsayawa tare da yaransu a lokacin da suke karatu da waya, ta bayyana cewa a matsayinta na uwa, a duk lokacin da yaronta zai yi karatu, takan tsaya a kusa da shi domin sa ido.
A cewarta, babban abu da ya kamata a ce ana yi wa yara shi ne wa'azi kan illolin intanet, ma'ana a nuna musu illoli da kuma faɗa musu abin da bai kamata su yi ba.
Ta bayyana cewa dan autanta shekararsa 13, kuma idan zai yi karatu tana zama tare da shi ta taimaka masa wurin neman ilimi ana wasa da dariya.
BBC ta kuma tattauna da wata uwa wadda ba ta so a bayyana sunanta inda ta bayyana cewa, tana ƙokarin duba wayoyin yaranta domin sanin waɗanne irin manhajoji ne a ciki da za su iya kai su hanyoyin da ba su da amfani.
Ta kuma bayyana cewa takan saka kanta a ɓoye cikin dandalin ajin yaranta na whatsapp domin sanin me suke tattauna wa a ciki.