Waɗanne tambayoyi kuke da su kan Masarautar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar?

Masarautar Katsinan Maraɗi

Asalin hoton, Abdou Halilou/BBC

An wallafa

Idan za ku iya tunawa a baya-bayan nan BBC na yawan kawo muku maƙalu kan tarihin wasu manyan Masarautun Ƙasar Hausa inda a baya muka kawo na Masarautar Borno da ta Sokoto da ta Kano da kuma ta Zazzau.

Kafin mu kara kawo na wasu masarautun a Najeriya, wannan karon za mu leƙa ne Jamhuriyar Nijar don tabo tarihin Masarautar Katsinan Maraɗi.

Sai ku aiko mana da tambayoyinku mu kuma za mu yi bincike sosai don amsa muku.