Buhari na bikin cika shekara ɗaya a wa'adi na biyu

An wallafa

Gwamnatin Muhammadu Buhari na bikin cika shekara guda da hawa kan karagar mulki bayan sake zaɓensa a shekara ta 2019.

Duk da ɗumbin ƙalubalan da suka dabaibaye ƙasar a shekarun baya-bayan nan, gwamnatin Buhari na bugun ƙirjin ta cimma wasu nasarori.

Ko da yake, wasu da dama ciki har da 'yan adawa na ganin nasarorin gwamnatin Buhari wanda aka fara zaɓa a shekara ta 2015 ba su taka kara sun karya ba.

Mun tsakuro muku kaɗan daga cikin nasarorin da gwamnatin ta ce ta samu cikin wata muƙala da ta fitar don bikin cika shekara guda a wa'adi na biyu kan mulki.

Ababen more rayuwa

Manyan ayyukan layin jirgin ƙasa da ta gada daga gwamnatin da ta gabata ciki har da Abuja Metro Rail da layin dogo na Abuja zuwa Kaduna da kuma layin jirgin ƙasa mai tsawon kilomita 327 daga Itakpe zuwa Ajaokuta zuwa Warri wanda aka fara tun 1987 amma sai bana aka kammala shi.

Hukumar kula da dukiyar zuba jari ta Najeriya a watan Maris ta zuba $11m wajen kafa cibiyar kula da masu cutar kansa ta zamani a asibitin koyarwa na Jami'ar Lagos kuma ta fara aiki a 2019.

Ana ci gaba da aiki kan cibiyoyin duba marasa lafiya a asibitin koyarwa na Aminu Kano da kuma cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Umuahia a kan kuɗi $5m.

An tsara kammala aikin sabbin tashoshi a filayen jirgi na Kano da Lagos a 2020. Kuma gwamnati ta ce za a kammala aikin sake gina hanyar sauka da tashin jirage bana a filin jirgin sama na Enugu

Bangaren tsaro

Hukumomin tsaron Najeriya sun yi gagarumin haɓaka tasirinsu a faɗin ƙasar ta hanyar shirye-shiryen tabbatar da tsaro irinsu Operation Whirl Stroke a shiyyar arewa ta tsakiya da Operation Ex-Swift Response a yankunan kan iyakokin ƙasa, cewar sanarwar.

Sabbin sansanonin aikace-aikacen soja da sansanonin sojin sama na kai ɗauki cikin hanzari da makarantun horas da sojojin ƙundumbala da sauransu.

Tura dakarun soja na musamman zuwa wasu yankunan ƙasar.

Gwamnatin Buhari ta kuma ta ƙara yawan kuɗaɗen da ake kashewa wajen sayen makamai da kayan yaƙi ta hanyar yarjejeniyoyin bunƙasa ayyukan soja da gwamnatocin ƙasashen Amurka da China da Rasha da Pakistan da sauransu.

A cewarta hakan ya taimaka wajen cire tsarin 'yan kwangila mai matuƙar tsada.

Ta ce ko a watan Afrilun 2020 rukunin farko na motocin soja 17 da suka hadar da tankokin yaƙi da tankokin atilare sun isa ƙasar daga China, don yaƙi da ƙungiyar Boko Haram.

Ta ce a tsawon shekara biyar na mulkin Shugaba Buhari, rundunar sojin saman Nijeriya ta sayo sabbin jiragen yaƙi 22.

Kuma tana sa ran karɓar ƙarin wasu 16 ciki har da ƙirar Super Tucano guda 12 waɗanda ta siya daga gwamnatin Amurka kuma za a fara kawo su ƙasar a shekara ta 2021.

Shugaba Buhari ya kuma farfaɗo da Ma'aikatar kula da 'Yan sanda a bara, don tafiyar da tsare-tsaren aiwatarwa da bunƙasawa da kuma inganta tsaron cikin gida a Najeriya.

Haka zalika, Shugaba Buhari ya amince da ɗaukar sabbin 'yan sanda 10,000 duk shekara, in ji gwamnatin Najeriya.

Shugaban ya kuma sa hannu kan wani ƙuduri da ya zama doka a shekara ta 2019 don kafa wani asusun amintattu na rundunar 'yan sanda wanda zai yi matuƙar inganta samar da kuɗi ga ayyukan 'yan sanda.

Muhammadu Buhari ya kuma amince da aiwatar da sabon ƙunshin albashin sojoji da 'yan sanda.

Ga kuma sake farfaɗo da rundunar haɗin gwiwar sojojin ƙasashen yankin Tafkin Chadi MNJTF da nufin yaƙar laifuka tsakanin kan iyakokin ƙasashe da kuma ayyukan ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram.