Covid-19: Hotunan yadda aka yi bikin sallah cikin kulle a Afirka

An wallafa

Musulmai a fadin Afirka da sauran sassan duniya na murnar ƙaramar sallah, wadda ake gudanarwa a farkon watan Shawwal.

Wasu 'yan uwa Musulmai kenan ke rungume juna a wajen wani masallaci da ke a Nairobi babban birnin Kenya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu Musulmai kenan ke rungume juna a wajen wani masallaci da ke a Nairobi babban birnin Kenya
An kulle dukkan masallatai a ƙasar Kenya sakamakon annobar korona, wadannan mutanen na gudanar da Sallar Idi a harabar gidansu..

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An kulle dukkan masallatai a ƙasar Kenya sakamakon annobar korona, wadannan mutanen na gudanar da Sallar Idi a harabar gidansu..
Wadannan mutanen sun samu hanyar da suka bi suka shiga masallaci a Nairobi domin su yi sallah amma sun bayar da tazara tsakaninsu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wadannan mutanen sun samu hanyar da suka bi suka shiga masallaci a Nairobi domin su yi sallah amma sun bayar da tazara tsakaninsu.
An buƙaci musulmai a Najeriya da su gudanar da Sallar Idi a gida amma duk da haka wasu sun taru a jihar Nasarawa a wajen wani masallaci inda suka gudanar da sallah.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An buƙaci musulmai a Najeriya da su gudanar da Sallar Idi a gida amma duk da haka wasu sun taru a jihar Nasarawa a wajen wani masallaci inda suka gudanar da sallah.
Wasu Musulmai kenan a jihar Ogun suke gudanar da sallah inda suke bayar da tazara a tsakaninsu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu Musulmai kenan a jihar Ogun suke gudanar da sallah inda suke bayar da tazara a tsakaninsu
A duk lokacin ƙaramar sallah a Najeriya, ana saka wa yara sabbin kaya domin zuwa masallaci. An ɗauki wadannan yaran ne kan achaɓa bayan Sallar Idi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A duk lokacin ƙaramar sallah a Najeriya, ana saka wa yara sabbin kaya domin zuwa masallaci. An ɗauki waɗannan yaran hoto ne kan achaɓa bayan Sallar Idi...
Wani yaro kenan yake alwala domin gudanar da sallah, an dauki wannan hoton ne a a wajen wani masallaci.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani yaro kenan yake alwala domin gudanar da sallah, an dauki wannan hoton ne a wajen wani masallaci.
Gwamnatin Sudan ta saka dokar hana taruwar jama'a, amma da alama wasu mutanen da ke zaune a Khartoum babban birnin ƙasar sun bijre wa wannan doka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Gwamnatin Sudan ta saka dokar hana taruwar jama'a, amma da alama wasu mutanen da ke zaune a Khartoum babban birnin ƙasar sun bijire wa wannan doka..
Amma da sauki wasu daga cikinsu sun saka takunkumin rufe fuska.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Amma da sauki wasu daga cikinsu sun saka takunkumin rufe fuska....
Presentational white space
A Arewacin Afirka, yanayin nasu daban ne - da komai lafaiya ƙalau da tuni Masallacin Zitouna da ke a ƙasar Tunisia ya cika maƙil da mutane lokacin Sallar Idi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Arewacin Afirka, yanayin nasu daban ne - da a ce komai lafiya ƙalau da tuni Masallacin Zitouna da ke a ƙasar Tunisia ya cika maƙil da mutane lokacin Sallar Idi....
Haka zalika masallacin Al-Azhar da ke birnin Alƙahira da ke Masar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Haka zalika masallacin Al-Azhar da ke birnin Alƙahira da ke Masar.

Duka hotunan suna da haƙƙin mallaka