Coronavirus a Afirka: Kalubalen da wasu kasashe suke fuskanta

Medical staff at the Chandaria Health Centre try on face shields in Nairobi, Kenya - 14 May 2020

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargaɗin cewa a kalla mutum miliyan 250 a Afirka za su iya kamuwa da cutar korona a shekarar farko ta bullar cutar.

Hukumar ta yi hasashen cewa tsakanin mutum 150,000 zuwa 190,000 za su iya mutuwa sakamkon cutar.

Duk da cewa Afirka na da ƙasa da mutum 100,000 da suka kamu da cutar amma a halin yanzu, ƙwararru daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun yi gargaɗin cewa nahiyar za ta ci gaba da samun ɓarkewar cutar zuwa shekaru masu zuwa - haka zalika masana kiwon lafiya sun bayyana cewa a ƙoƙarin da ake yi na shawo kan cutar ya sa aka yi biris da ɓangaren kiwon lafiya.

A nan, wasu daga cikin masu bada rahotanni na BBC sun bayyana wasu abubuwa dangane da cutar a Afirka.

Short presentational grey line

Mai Yiwuwa 'yan Congo na 'dauke da cutar ba tare da sun sani ba'

Daga Emery Makumeno, Kinshasa

A staff member of the Congolese Ministry of Health prepares the sampling equipment to perform a COVID-19 test at a private residence in Goma, northeastern Democratic Republic of Congo, on March 31, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Congo na fama da korona da kuma Ebola

Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo ta tabbatar da samun mutum na farko mai ɗauke da cutar korona a farkon watan Maris, sai dai wani likita a Kinshasa yana da yaƙinin cewa cutar ta ɓulla tun kafin lokacin.

''Cikin watan Disamba da Janairu, bazan iya tunawa da yawan mutanen da suka zo suna tari da masassara da ciwon kai ba,'' a cewar likitan, inda yake bayyana alamomin cutar korona kamar yadda WHO ta bayyana.

''Ina da yakinin cewa mu malaman lafiya tuni muka kamu da korona ba tare da mun sani ba, amma tuni garkuwar jikinmu ta samar da kariya daga ciwon,'' in ji shi.

Amma sakamakon karancin kayan gwaji, mutane kadan ne aka yi wa gwaji domin duba cewa ko suna dauke da cutar korona.

Kasashen da suke da kyakyawan tsari na gwaji kamar Korea ta Kudu da kuma Jamus, tuni aka yi gwaji ga kashi daya cikin 100 na mutanen kasashen, kamar yadda wata mujallar kiwon lafiya ta Birtaniya ''The Lancet'' ta bayyana.

A halin yanzu, kasar Congo na da mutum 1,600 da suka kamu da cutar - ita ce ta tara a yawan cutar korona a nahiyar Afirka.

Presentational grey line
Children wait to be registered before a measles vaccination at a centre in Mbata-Siala, near Seke Banza, western DR Congo on March 3, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Short presentational grey line

Asibitin Kenya na da 'karancin marasa lafiya da gawarwaki masu yawa'

Daga Mercy Juma, Nairobi

A barber tends to a client while wearing personal protective equipment (PPE) donated by a local youth group comprised of some entrepreneurs who have lost their livelihoods due to the economic slump caused by countrywide restrictions imposed on movement of people and goods, in a bid to curb the spread of the COVID-19 coronavirus, who manufacture personal protective equipment (PPE) in a shed in Waithaka, a suburb of Nairobi on May 14, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, To cover your face become the norm in Kenya

An samu karuwar kusan kashi 40 cikin 100 na masu cutar lumfashi da suka hada da tarin lala da ciwon namoniya da ciwon asma a wani babban asibiti da ke Nairobi babban birnin kasar Kenya.

Sai dai an samu raguwar irin wadannan cutuka tun tsakiyar watan Maris, in ji wani likita wanda ya yi wa BBC karin bayani amma ya bukaci a sakaya sunansa sakamakon bai da hurumin magana da 'yan jarida.

Daya daga cikin dalilan shi ne gwamnatin kasar ta saka dokar hana fita daga safew zuwa dare a yunƙurinta na shawo kan yaduwar cutar.

Wannan ya jawo raguwar mutanen da ake kai wa asibiti da dare amma kuma yawan wadanda ake kai wa dakin ajiya gawarwaki ya ƙaru.

Someone in quarantine in Kenya holding up a "Please help us" sign - April 2020

Asalin hoton, AFP

Ya bayyana cewa jama'a da dama sun rinƙa gudun zuwa asibiti sakamakon kada a yi musu agwaji a ce suna da korona a kai su wurin killacewa.

Hakan ya faru sakamakon killacewa a Kenya na da rudani, inda gwamnati ke tilasta wa wadanda ake zargi da korona su biya kudin killacewarsu.

Jama'a na biyan daga dala 20 zuwa 100 a wuraren killacewa a duk rana, wurin da aka ajiyeb mutum ke nuna irin kudin da zai biya.

Presentational grey line
Presentational grey line
Short presentational grey line

'Yawan marasa lafiya da yawan mace-mace' a arewacin Najeriya

Daga Ishaq Khalid, Abuja

A patient who is suspected of suffering from COVID-19 coronavirus undergoes testing at the University of Maiduguri Teaching Hospital isolation centre on May 10, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Akwai rahotanni da ke nuna cewa jama'a da dama na rashin lafiya da kuma mutuwa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya tun bayan da aka samu bullar cutar korona kusan watanni uku da suka wuce.

Ba abin mamaki bane idan aka ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙara tsawaita dokar kulle a jihar zuwa karshen wata.

Wani mai aikin gina ƙabari da ke a maƙabartar Abatuwa ya shaida cewa bai taba ganin irin haka ba, tun bayan cutar kwalara da iyayansa suka ba shi labari da ta barke shekaru 60 da suka gabata.

Farfesa Baba Shani - shugaban tsangayar koyar da aikin likitanci wanda yake a asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke jihar ya shaida wa BBC cewa suna duba marasa lafiya masu cututtuka kamar asma da nimoniya da tarin lala da ciwon kirji da ciwon maƙogwaro.

Farfesan ya bayyana cewa an samu ƙaruwa da kusan kashi 40 zuwa 45 cikin 100 na masu fama da matsalar numfashi a asibitin a watanni uku da suka wuce.

Taxi in Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Ya kuma alakanta hakan da kulle asibitoci da dama na jihar musamman masu zaman kansu sakamakon ƙarancin kayayyakin kariya. Wannan ne ya sa marasa lafiya ke naman magani a asibitin koyarwa na Aminu Kano.

Baba Shani ya bayyana cewa wasu daga cikin wadanda aka samu da matsalar numfashi an masu gwaji an ga suna da coronavirus inda aka mayar da su wuraren killace masu cutar korona.

Presentational grey line
Presentational grey line
Short presentational grey line

'Ƙananan alamomin cutar' a Ethiopia

Daga Klakidan Yibelta, Addis Ababa

Health Extension workers of the Ministry of Health measure the tempreature of a girl during a door to door screening to curb the spread of the COVID-19 coronavirus in Addis Ababa, Ethiopia, on April 20, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Ana yawan samun cututtuka masu alaƙa da numfashi a Ethiopia, kasar da ita ce ta biyu a yawan jama'a a nahiyar Afrika da ke da sama da mutum miliyan 100.

Bincike ya nuna cewa cutuka masu alaƙa da numfashi ne na uku a jerin abubuwan da ke sanadin mutuwar mutane a kasar.

Ɓarkewar cutar korona bai sa an samu ƙaruwar masu ɗauke da cutuka da ke da alaka da numfashi wadanda ake kwantar da su a asibiti ba.

Wani Likita a Adis Ababa ya shaida wa BBC cewa yana ta neman alamomin cutar korona a kasar amma bai ga wani abu wanda tun can dama bai saba gani ba.

Presentational grey line
Presentational grey line

Ba a samu ƙaruwar masu nimoniya ba da sauran cutuka ba da korona ke ƙara jawo wa ba.

Short presentational grey line
Banner